
A ranar Litinin Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kai wata ziyara ta ba-zata a sakatariyar gwamnatin jihar domin duba yadda ma’aikata ke gudanar da ayyukansu, inda ya samu mafi yawancin ma’aikata ba su halarta ba.
A yayin ziyarar, gwamnan ya tarar da ofisoshin manyan jami’an sakatariyar da dama a kulle, yayin da kuma ya gano cewa da yawa daga cikin manyan ma’aikata ba su halarci wuraren ayyukansu ba, duk da cewa lokacin ya kai ziyarar kusan ƙarfe 11:00 na safe ne.
A cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Namadi yana zagayawa ma’aikatu daban-daban, yana buɗe ofisoshi tare da gano cewa yawancinsu babu ma’aikata a ciki, sai kaɗan daga cikin masu gadi da ‘yan aike.
Ana sa ran wannan ziyarar za ta ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aiki da tabbatar da ɗa’a a aikin gwamnati a jihar tsakanin jami’an gwamnati.
