Matar Sarkin Kabi Muhammadu Mera ta rasu

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Allah ya yi wa Hajiya Halima ɗaya daga cikin matan Marigayi Sarkin Kabi Muhammadu Mera rasuwa. Hajiya Halima ta rasu a garin Argungu safiyar Laraba ɗin nan bayan fama da rashin lafiya, an kuma gudanar da sallar jana’izar a fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu inda aka sami halartar mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi, kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomin masarautar Argungu, waƙilin Sarkin Gwandu Sarakuna, ƴan kasuwa, ƴan siyasa da kuma jami’an gwamnati.

Mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa wace ba za a manta da ita ba. Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan ta da rahama mu kuma idan tamu ta zo ya sa mu mutu muna Musulmi masu imani.

Hajiya Halima ta bar ƴaƴa da jikoji da dama da suka haɗa da Alhaji Isah Muhammad Mera wanda yana ɗaya daga cikin Kwamishinoni a gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris.

By ukarofi

Leave a Reply