Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya kamfanonin samar da wutar lantarki guda takwas (GenCos) jimillar Naira biliyan 333 a matsayin kashin farko na shirin biyan tarin basussukan da ɓangaren wutar lantarki ke bi.
An bayyana cewa kuɗin sun shafi tashoshin samar da wutar lantarki guda 17 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga shirin.
Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Makamashi, Olu Verheijen, ce ta bayyana hakan ranar Talata yayin taron masu zuba jari da aka shirya domin ƙaddamar da kashi na biyu na takardun bashi na Shirin Gyaran Kuɗaɗen ɓangaren Wutar Lantarki na Shugaban ƙasa (PPSFRP), wanda darajarsa ta kai naira biliyan 729.
Ta ce, kashi na farko na shirin ya cika alƙawarin da aka ɗauka, inda Gwamnatin Tarayya ta fitar da kusan naira biliyan 501 a watan Fabrairun 2026 domin fara biyan basussukan da aka tantance.
A cewarta, daga cikin wannan kuɗi, naira biliyan 300 an biya su kai tsaye, yayin da kusan naira biliyan 201 aka biya ta hanyar takardun bashi, lamarin da ya rufe kusan kashi 22 na basussukan da aka amince da su a ƙarƙashin yarjejeniyoyin da aka ƙulla.
Verheijen ta ce, zuwa yanzu an riga an biya naira biliyan 333.12 ga kamfanonin samar da wutar lantarki guda takwas da suka shiga shirin. Ta kuma bayyana cewa gwamnati ta cika alƙawarinta na biyan kuɗin ribar farko ta takardun bashin, inda aka biya kusan naira biliyan 63.5 a ranar 14 ga watan Yuli, 2026.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawarar ta jaddada cewa amincewa da gaskiyar gwamnati da kuma cika alƙawura na daga cikin muhimman abubuwan da ke jawo masu zuba jari masu zaman kansu. Ta ce, gwamnati dole ne ta nuna cewa tana mutunta yarjejeniyoyi, tana cika alƙawuran da ta ɗauka, kuma tana gudanar da manufofi masu tabbas kafin masu zuba jari su amince da ita. A cewarta, wannan shi ne abin da shirin PPSFRP ya fara tabbatarwa, domin samun kuɗaɗen zuba jari ba ya farawa daga kasuwannin kuɗi kawai, sai gwamnati ta fara nuna gaskiya da mutunta yarjejeniyoyi.
Verheijen ta ce, wannan sabon amincewar da aka samu ya fara haifar da sauye-sauye masu kyau a dukkan sassan masana’antar wutar lantarki. Ta bayyana cewa, kamfanonin da suka shiga shirin sun fara biyan masu samar musu da iskar gas, cibiyoyin ba da rance da kuma kamfanonin kula da kayan aiki, waɗanda a baya suka daɗe ba tare da an biya su ba.
Ta ƙara da cewa irin yadda masu zuba jari suka nuna sha’awa wajen sayen takardun bashin kashi na farko ya nuna ƙarin yarda da shirin da kuma sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya.
A cewarta, sabon kashin takardun bashin zai taimaka wajen ci gaba da biyan tsofaffin basussukan da aka tabbatar, inganta yawan kuɗaɗen da ke zagayawa a ɓangaren wutar lantarki da kuma samar da ingantaccen tushe da zai jawo zuba jarin masu zaman kansu na dogon lokaci. Ta ce, masu zuba jari ba wai takardar bashi kawai suke saya ba, suna kuma zuba jari ne a wani shiri da aka tsara domin dawo da tsarin biyan kuɗi yadda ya kamata, ƙarfafa harkokin kuɗaɗen bangaren wutar lantarki da kuma bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.
Verheijen ta jaddada cewa manufar shirin ba ta tsaya ga gyaran bayanan kuɗi ko kasuwar hannayen jari ba kawai, domin babban burinsa shi ne inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyar samar da ingantacciyar wutar lantarki. Ta ce, hakan zai ba ɗalibai damar ƙarin lokacin karatu, ya rage wa masu ƙananan sana’o’i dogaro da janareto masu amfani da dizal mai tsada, tare da ƙara ƙarfin masana’antu saboda samun ingantacciyar wutar lantarki mai araha.
A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na fitar da kashi na biyu na takardun bashi da darajarsu ta kai kusan naira biliyan 729, domin ci gaba da biyan basussukan da aka tabbatar ana bin kamfanonin samar da wutar lantarki.
Shirin na cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin ƙarfafa kuɗaɗen da ke zagayawa a ɓangaren wutar lantarki, ƙara amincewar masu zuba jari da kuma shimfiɗa tubalin jawo jarin masu zaman kansu cikin masana’antar wutar lantarki ta Nijeriya.
