Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano
A ƙoƙarinta na tallafa wa gwamnatin jihar Jigawa wajen yaƙi da sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba, ƙaramar Hukumar ɓaɓura ta gargaɗi manoma da makiyaya da su guji wannan dabi’a da ke haddasa lalacewar muhalli da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban ƙaramar Hukumar Babura, Alhaji Muhammad Hamisu Garu, ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummomin da guguwar iska da ruwan sama suka shafa a sassa daban-daban na karamar hukumar.
Ya ce gwamnatinjihar karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi na daukar matakai domin dakile matsalar lalacewar muhalli, wadda ke kara haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, musamman a lokacin damina.
Alhaji Hamisu Garu ya bukaci manoma da makiyaya da su guji sare itatuwa ko kwashe dazuka domin yin noma ba tare da izinin hukumomi ba, yana mai cewa hakan na janyo matsaloli masu yawa da suka hada da kwararowar hamada da karuwar illar iska mai karfi.
Ya danganta yawaitar asarar gidaje da rayuka da guguwar iska ta haddasa da lalacewar muhalli sakamakon sare itatuwa a yankin.
Shugaban karamar hukumar ya kuma yi kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk wanda suka gani yana sare itatuwa ko lalata dazuka ba bisa ka’ida ba, domin daukar matakin da ya dace.
A cewarsa, sama da gidaje 150 ne guguwar iska da ruwan sama suka lalata a sassa daban-daban na karamar hukumar, ciki har da Babbar Kwalejin Koyon Ayyukan Lafiya da ke Anguwar Zoma a Babura.
Ya ce guguwar ta lalata rufin dakunan kwanan dalibai, wasu ofisoshin malamai da gidajensu, tare da shafar gidaje da dama a garuruwan Adiware da Anguwar Mai Kalangu.
Alhaji Hamisu Garu ya yi alkawarin isar da koken wadanda abin ya shafa ga Gwamnatinjihar Jigawa domin a samar musu da tallafin da ya dace.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya mayar wa wadanda abin ya shafa abin da suka rasa da mafificin alheri.
A ziyarar jajen, shugaban karamar hukumar ya samu rakiyar Sakataren Karamar Hukumar da wakilai daga hukumomin noma da kare muhalli na Jihar Jigawa.
Ya kuma tunatar da al’umma hasashen da hukumomin kula da yanayi suka yi cewa akwai yiwuwar samun mamakon ruwan sama da ambaliya a bana, saboda haka ya bukaci jama’a su dauki matakan kariya tare da kauce wa ayyukan da ke lalata muhalli domin rage illolin sauyin yanayi.
