2027: Fubara ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da ɗan takarar Wike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana goyon bayansa ga takarar wa’adi na biyu ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da ɗan takarar gwamnan jihar, Kingsley Chinda, a babban zaɓen shekarar 2027.

Fubara ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin bikin aza harsashin ginin Riɓen Medical Industries Project a birnin Fatakwal.

Ya ce sabanin siyasa da ya raba masu ruwa da tsaki a jihar ya zo ƙarshe, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a fifita zaman lafiya da haɗin kai maimakon rikicin siyasa.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya koma cikin Rainbow Coalition, wata ƙungiyar siyasa da tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Cif Nyesom Wike, ke jagoranta domin ci gaban jam’iyyar APC a jihar Ribas.

“Mun samu zaman lafiya a jihar, kuma ina goyon bayan Rainbow Coalition. Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne shugabanmu, kuma shi ne muke marawa baya. Na koma cikin iyalinmu. Lokacin rikici ya wuce, yanzu lokaci ne na zaman lafiya, kuma wannan zaman lafiya zai kai mu wani sabon mataki,” in ji Fubara.

Ya kuma buƙaci magoya bayansa su mara wa dukkan ‘yan takarar Jam’iyyar APC baya a zaɓen 2027, tare da gujewa duk wani abu da zai iya haddasa rarrabuwar kai.

Da yake jawabi kan aikin Riɓen Medical Industries Project, Fubara ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin zuba jari da zai bunƙasa masana’antu, samar da dubban ayyukan yi da kuma inganta harkar kiwon lafiya a jihar.

Sai dai ya gargaɗi masu zuba jarin da su cika alƙawuran da suka ɗauka, yana mai tunatar da yadda wasu masu zuba jari a baya suka yi watsi da ayyukansu, lamarin da ya jawo shari’o’i na tsawon lokaci.

Ya nuna ƙwarin gwiwa cewa sabbin masu zuba jarin za su farfaɗo da tsohuwar cibiyar Integrated Medical Industries (IMI), tare da kammala matakin farko na aikin cikin watanni uku.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummomin da ke yankin da kuma shugabannin ƙaramar Hukumar Obio/Akpor da su ba aikin cikakken goyon baya tare da samar da yanayin zaman lafiya domin gudanar da shi.

A cewarsa, aikin haɗin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Ribas da kamfanin Enbay Pharmaceutical Industries Ltd, wanda manufarsa ita ce sake gina tsohuwar cibiyar IMI ta zama babbar masana’antar sarrafa magunguna.

Ana sa ran masana’antar za ta riƙa samar da nau’o’in magunguna, kapsul na gelatin, ruwan allura (IV infusions) da sinadaran asali na magunguna (Active Pharmaceutical Ingredients), domin ƙarfafa samar da magunguna a cikin gida, rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje, da bunƙasa sarkar kiwon lafiya ta Nijeriya.

Haka kuma ana sa ran aikin zai samar da dubban ayyukan yi kai tsaye da kuma a kaikaice, ya jawo sababbin masu zuba jari, tare da mayar da Jihar Ribas cibiyar masana’antar magunguna a Nijeriya da yankin Afirka ta Yamma.

By ukarofi