Andy Burnham ya zama Firaminista na shida da ya shiga gidan gwamnati da ke layin Downing a ranar Litinin, tun daga shekarar 2016, bayan da Sarkin Birtaniya, Charles na uku, ya ba shi amanar kafa sabuwar gwamnati.
Kamfanin dillancin labarai na AFP, kamar yadda Channels TV ya ruwaito, ya ce Burnham mai shekaru 56 zai maye gurbin Keir Starmer, wanda ya yi murabus daga mukamin Firaminista da shugaban Jam’iyyar Labour bayan fuskantar suka da jerin matsalolin siyasa.
Ana sa ran Burnham zai gabatar da jawabinsa na farko a gaban gidan gwamnatin Downing Street bayan Keir Starmer ya yi bankwana da ofishinsa.
A cikin jawabin, zai bayyana manyan tsare-tsarensa na dawo da amincewar jama’a ga gwamnati da kuma samar da ingantaccen shugabanci.
A wata hira da jaridar The Times, Burnham ya ce yana son kawo ƙarshen shekaru na rikice-rikicen siyasa da Birtaniya ta fuskanta, yana mai cewa hanyoyin da aka bi a baya ba su haifar da sakamakon da ake buƙata ba, saboda haka gwamnatinsa za ta ɗauki sabuwar hanya.
Manyan ƙalubalen da ke gabansa sun haɗa da bunƙasa tattalin arziƙi, rage tsadar rayuwa, yawan bashin gwamnati, da kuma magance matsalar baƙin haure masu shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Burnham ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan saka hannun jari, inganta tattalin arziki da rage matsin tattalin arziƙin da al’umma ke fuskanta.
Kafin hawansa kan mulki, Burnham ya kasance magajin garin Greater Manchester, sannan ya taɓa zama ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya da kuma minista a gwamnatocin tsoffin firaministoci Tony Blair da Gordon Brown.
