Na zo domin na yi tasiri, ba don cike gurbi ba, inji Oyinkansola, sabuwar shugabar NBA

Spread the love

“Takun mace ta farko da aka zaɓa kai tsaye ta jagoranci ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya”

Daga AISHA ASAS

Akwai kwanakin da ba su buƙatar shela domin a san cewa sun bambanta da sauran kwanaki. Kwanaki ne da tarihi kan buɗe sabon shafi, al’umma kuma ta tsaya ta na kallon yadda sabon labari ke samun gurbi a cikin littafin tarihi. Irin waɗannan kwanaki ba su sauya labarin mutum ɗaya kaɗai; su na sauya yadda ake kallon abin da zai yiwu a gaba.

A ranar da aka sanar da sakamakon zaɓen shugabancin ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), ba wai kawai an bayyana sunan wadda ta yi nasara ba. An kuma rufe wani babi da ya shafe fiye da shekaru talatin ana jiran wanda zai rubuta ƙarshensa. Wato shugabancin maza a wannan ɓangare. 

Lokacin da aka ayyana Oyinkansola Badejo-Okusanya a matsayin shugabar NBA da aka zaɓa kai tsaye, a ɓangaren dubban lauyoyi sun ga sakamakon zaɓe ne. Amma ga masu kallon tarihi, wannan rana ta fi zama alamar sauyin zamani a cikin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwararru mafi tasiri a Najeriya.

Abin da ya sa nasarar ta bambanta shi ne, ba wai kasancewarta mace ta farko da ta jagoranci NBA ba, domin an taɓa samun mace a wannan kujera. Sai dai, mace ta farko da ta samu wannan matsayi ta hanyar cikakken zaɓe. Wannan bambanci ne ya sanya sunanta shiga cikin jerin mutanen da suka sauya alƙiblar tarihi ta hanyar aiki da jajircewa.

Sai dai duk wanda ya kalli wannan nasara a matsayin abin da ya faru cikin dare, zai ga ƙarshen tafiya ne kawai, ba tare da ya tambayi inda aka fara ba.

Kafin ranar da aka ɗaga hannunta a matsayin wadda ta yi nasara, akwai shekaru masu yawa na gwagwarmaya; shekaru da ta fi zaɓar aiki fiye da fitowa a kanun labarai, ta yi hidima a kwamitoci, ta fuskanci ƙalubale, sannan ta ci gaba da gina kanta cikin jajircewa.

Sunna ce ta rayuwa cewa, wasu nasarori ba sa bayyana a ranar da aka samu su kaɗai. Wasu shekaru ne suke rubuta su kafin wata rana ta zo ta bayyana abin da aka daɗe ana ginawa.

A wannan makon, shafin Gimbiya ya sake zaƙulo muku rayuwar wata baiwar Allah wadda ta nuna cewa shugabanci ba ya fara wa daga ranar da aka rantsar da mutum. Yana farawa ne tun lokacin da mutum ya yanke shawarar gina kansa da ilimi, ƙwarewa, mutunci da hidimar jama’a.

Tafiyar Oyinkansola Badejo-Okusanya ba kawai labarin mace da ta kai wani matsayi ba ce; labari ne na yadda dogon shiri, jajircewa da amincewa da kai za su iya haifar da canji.

Matakin farko bayan kammala karatun lauya ya kai Oyinkansola Badejo-Okusanya zuwa Olaniwun Ajayi LP, ɗaya daga cikin manyan gidajen lauyoyi mafi daraja a Najeriya.

A irin wannan muhalli ne ake gwada ƙwarewar lauya fiye da abin da ke rubuce a takardar shaidar karatu. Ana auna mutum da zurfin tunaninsa, iya nazarin matsala, ƙarfin hujja da kuma yadda yake gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa.

A nan ne Oyinkansola ta fara gina sunan da daga baya ya zama abin girmamawa a fannin shari’a. Ba ta kasance cikin masu neman fitowa a idon jama’a ba; ta fi mayar da hankali kan aikinta, tana gina amincewa ta hanyar ƙwarewa, mutunci da jajircewa.

Wannan amincewar da ta samu tun farkon aikinta ce ta sa aka fara kallonta a matsayin lauya mai damar bayar da gudunmawa fiye da gudanar da shari’o’i a kotu.

Saboda haka, lokacin da gwamnatin Jihar Legas ta fara ɗaukar matakan sake fasalin ɓangaren shari’a, sunanta ya kasance cikin waɗanda aka ga sun dace da wannan aiki.

A shekarar 2007, tsohon gwamnan jihar, Babatunde Raji Fashola, ya naɗa ta Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Gyaran Sashen Shari’a.

Ta yi aiki a ƙarƙashin Babban Lauyan Jihar Legas kuma Kwamishinan Shari’a na lokacin, Olasupo Shasore (SAN), inda ta kasance cikin tawagar da ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi tsarin shari’a a jihar.

Ayyukan da ta gudanar a wannan lokaci ba su tsaya kan shirya takardun gwamnati ko ba da shawarwari kawai ba. Ta kasance cikin masu tsara hanyoyin da za su inganta yadda jama’a ke samun adalci, tare da tallafa wa sauye-sauyen da suka shafi Office of the Public Defender, da kuma inganta tsarin kula da waɗanda ake tsare da su kafin a yanke musu hukunci.

Ko da yake irin waɗannan sauye-sauye ba sa yawan fitowa a kanun labarai, suna daga cikin abubuwan da ke taimaka wa wajen inganta tsarin shari’a da sauƙaƙa samun adalci.

A wannan matsayi ne Oyinkansola ta ƙara fahimtar cewa doka ba ta tsaya a cikin kotu kaɗai ba, tana da alaƙa da yadda gwamnati ke tsara manufofi, yadda ake kare haƙƙin jama’a, da kuma yadda ake gina tsarin da zai bai wa jama’a damar samun adalci cikin sauƙi.

Shekaru huɗu bayan haka, aka sake ba ta wani nauyi. Daga shekarar 2011 zuwa 2015 ta yi aiki a matsayin ‘General Counsel’ ga Gwamnan Jihar Legas, inda ta kasance cikin masu ba da shawara kan muhimman batutuwan gwamnati.

Ta bayar da gudunmawa a fannoni da suka haɗa da haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, dokokin sasanci, kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki, da kuma shirye-shiryen mallakar gidaje da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Waɗannan shekaru takwas da ta yi a cikin gwamnati sun ba ta damar kallon doka ta wata fuska dabam. Ba wai kawai a matsayin hanyar warware takaddama ba, har ma a matsayin kayan aiki na gina al’umma da samar da ingantattun manufofi.

Da wa’adin aikinta ya ƙare, ba ta tsaya wajen cin ribar mukaman da ta riƙe ba. Ta koma fagen aikin lauya da ƙarin gogewa, faɗaɗɗen hangen nesa da kuma ƙwarewar da ta samu daga haɗa aikin gwamnati da na zaman kansa.

A shekarar 2017 ta kasance cikin waɗanda suka kafa Africa Law Practice NG & Company (ALP NG & Co.), inda ta jagoranci ɓangaren da ke kula da shari’o’in kasuwanci da warware rikice-rikice.

A wannan matsayi, ta ba da shawarwari ga kamfanoni, hukumomin gwamnati da masu zuba jari kan manyan shari’o’in kasuwanci, sasanci da kuma rikice-rikicen da suka shafi harkokin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.

ƙwarewar da ta nuna ta ƙara mata matsayi a fannin sasanci na duniya. Ta zama Fellow na Chartered Institute of Arbitrators (CIArb), sannan aka amince da ita a matsayin ƙwararriyar mai sasanci ta CEDR.

Ta kuma yi aiki a kwamitin gudanarwa na reshen CIArb na Najeriya, inda ta jagoranci kwamitin shirya babban taron ƙungiyar har tsawon shekaru uku a jere.

Gudunmawarta ba ta tsaya nan ba. Ta kasance mamba a Hukumar Lagos Court of Arbitration, sannan ta taka rawa a ƙungiyar haɗin gwiwa tsakanin Nigeria Economic Summit Group da Majalisar Dokoki kan sake fasalin dokokin sasanci.

Masu bibiyar wannan fanni na ganin irin waɗannan gudunmawa sun taimaka wajen samar da Arbitration and Mediation Act 2023, dokar da ake kallon ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka samu a fannin sasanci a Najeriya cikin shekaru masu yawa.

Har ila yau, ta kasance mamba a wasu fitattun ƙungiyoyin ƙwararru na duniya, ciki har da London Court of International Arbitration (LCIA), International Council for Commercial Arbitration (ICCA), International Bar Association (IBA), Commonwealth Lawyers Association (CLA), International Federation of Women Lawyers (FIDA) da kuma African Women Lawyers Association (AWLA).

Duk da irin wannan matsayi da ta samu a matakin ƙasa da ƙasa, waɗanda suka san ta sun ce ba ta taɓa yanke alaƙarta da ƙungiyar Lauyoyin Najeriya ba.

Yayin da wasu ke kallon NBA a matsayin ƙungiyar da ake shiga ne idan ana neman muƙami, ita ta ɗauke ta a matsayin gida da ya kamata a yi wa hidima, ko da ba a gaban kyamarori ake yin wannan hidimar ba.

Wataƙila wannan ne ya sa tafiyarta cikin NBA ba ta fara daga neman shugabanci ba. Ta fara ne daga ayyukan da ba kasafai suke ɗaukar hankalin jama’a ba, amma su ne ke gina tubalin kowace babbar ƙungiya.

Tun kafin ta bayyana aniyarta ta neman shugabancin ƙungiyar Lauyoyin Najeriya, Oyinkansola Badejo-Okusanya ta shafe fiye da shekaru ashirin tana hidima a matakai daban-daban na ƙungiyar.

Wannan doguwar tafiya ce da ba ta ginu a kan neman suna ba, sai dai a kan kasancewa a duk inda aka ga akwai aikin da ya kamata a yi.

Ta fara daga matsayin Mataimakiyar Sakatariya ta reshen NBA na Legas, sannan ta kasance wakila a zaɓen ƙungiyar na shekarar 2006. Daga nan ta yi aiki a kwamitin kula da ginin reshen Legas, ta shiga kwamitocin fasaha na shirya tarukan shekara-shekara a zamanin shugabanni daban-daban, sannan ta jagoranci kwamitin shirya liyafar shekara ta reshen Legas tsakanin shekarun 2021 da 2022.

Waɗannan mukamai na iya zama ƙanana a idon waɗanda ke kallon shugabanci daga nesa. Amma ga masu fahimtar yadda manyan ƙungiyoyi ke tafiya, a irin waɗannan wurare ne ake gwada jajircewar mutum, juriyarsa da kuma yadda yake iya haɗa mutane masu ra’ayoyi mabambanta domin cimma buri guda.

A cikin shekarun da suka biyo baya, an ƙara ɗora mata wasu nauyi. Ta kasance mamba a Kwamitin Makomar Sana’ar Lauya, ta yi aiki a Kwamitin Binciken Taro, sannan aka naɗa ta mataimakiyar shugabar kwamitin shirya Babban Taron NBA na shekarar 2023.

Shekara guda bayan haka, aka ba ta jagorancin kwamitin shirya Babban Taron NBA na 2024, ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ƙungiyar ke gudanarwa a duk shekara.

Daga shekarar 2022 kuma, ta kasance mamba a Majalisar Zartarwa ta ƙasa ta NBA (NEC), inda ta ci gaba da taka rawa wajen tattauna manyan batutuwan da suka shafi makomar ƙungiyar da sana’ar lauya a Najeriya.

A watan Agustan 2024, NBA ta karrama ta da Presidential Medal of Serɓice, lambar yabo da ake bai wa mutanen da suka ba da gudunmawa ta musamman wajen ci gaban ƙungiyar.

Bayan shekara guda, a ranar 29 ga Satumban 2025, aka ɗaga ta zuwa matsayin Senior Adɓocate of Nigeria (SAN), matsayi mafi girma da lauya zai iya samu a Najeriya.

Ga mutane da dama, wannan mataki ya isa mutum ya tsaya ya waiwayi irin abin da ya gina tsawon shekaru. Amma ga Oyinkansola, kamar wani sabon babi ne kawai ke shirin buɗewa.

Lokacin da aka ware shugabancin NBA na shekarar 2026 zuwa yankin Yammacin Najeriya, sunanta ya shiga cikin waɗanda suka nuna sha’awar neman shugabancin ƙungiyar. A cikin ‘yan takarar uku, ita ce kaɗai mace.

Ba ƙaramin ƙalubale ba ne. Fiye da shekaru talatin sun shuɗe tun bayan da Priscilla Kuye ta jagoranci NBA a wani yanayi na musamman bayan wanda yake kan kujerar ya bar ofis.

Tun daga wancan lokaci, mata da dama sun yi yunƙurin kai wa wannan matsayi ta hanyar zaɓe, amma burinsu bai cika ba.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply