Makarantar Sautus Sunnah ta yaye ɗalibai a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Makarantar Sautussunnah International Comprehensive Secondary Schools Katsina ta gudanar da walimar yaye ɗalibai karo na tara.

An yaye ɗalibai 60 bayan sun kammala jarabawar ƙarshe ta WAEC da NECO a fannonin Kimiyya da fasaha da ɓangaren adabi da fasaha (Science da Arts).

Baya ga karatun zamani, makarantar ta ba da muhimmanci sosai ga tarbiyyar addinin musulunci da koyar da Alƙur’ani mai girma. Ɗaliban da aka yaye sun haɗa da: Ɗalibai 22 sun kammala hardar Alƙur’ani mai girma baki ɗaya, ɗalibai 15 sun haddace hizifi 50. Ɗalibai 13 sun harlddace hizifi 30,sai ɗalibai 10 da suka haddace hizifi 20.

A ɓangaren haddar Alƙur’ani, ɗaliba Asma’u Surajo Sukan, ita ce ta kasance fitacciyar ɗaliba saboda ƙwazon ta da hazaƙarta.

Haka kuma, a ɓangaren karatun zamani, ɗalibi Ridwan Abubakar Yuguda ne ya zama fitaccen ɗalibi bayan ya nuna ƙwazo da hazaƙa a karatunsa.

Makarantar ta taya dukkan ɗaliban da aka yaye murna tare da yi musu fatan samun nasara a matakai na gaba na karatu da rayuwa, tare da ci gaba da kasancewa jakadu nagari masu amfani ga addininsu da al’ummarsu.

Taron ya gudana ne a harabar makarantar dake cikin garin Katsina, inda ya samu halartar manyan baƙi daga wurare daban-daban da suka haɗa da limamai malamai shugabanni iyayen yara da sauran al’umma maza da mata.

By ukarofi

Leave a Reply