‘Yan bindiga sun halaka babban soja a yunƙurin garkuwa a Nasarawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin wasu ‘yan bindiga suka halaka wani babban jami’in soja mai suna Kanal Abdussalam A. Ude yayin wani yunƙuri na kai harin yin garkuwa a yankin Badna da ke Ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a yankin New Karu da ke iyaka da Birnin Tarayya Abuja, wanda da fari aka yi zaton ya faru ne a wani sashe na Abuja, kana daga bisani hukumomin tsaro suka tabbatar da cewa ya auku ne a Jihar Nasarawa.

A cewar rahotanni, maharan sun je gidan jami’in ne yayin da ake tsaka da zabga ruwan sama da nufin sace shi, inda ya yi musu gardama wanda a sanadiyyar haka ne suka yi ta harbinsa har ya rasu.

A washe garin ranar ne wani jagoran al’umma a yankin ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce gardamar da ya yi da maharan ne ta sa suka harbe shi.

Ya kuma ce, DPOn ‘yan sandan Kurudu ya halarci wajen da abin ya faru da kuma sanyawa a ɗauke gawar mamacin zuwa wajen adana gawarwaki.

Lamarin ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan Nijeriya, musamman hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Ana sa ran hukumomin tsaro za su ƙara kaimi wajen gudanar da bincike domin gano masu hannu a wannan hari tare da tabbatar da an gurfanar da su ga doka.

By Babaji

Leave a Reply