Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gidauniyar Dahiru Barau Mangal ta yi wa mutane 14,000 aikin udo tun bayan fara gudanar da aikin a Jihar Katsina.
Ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan yayin da ake ci gaba da aikin tiyatar ido kyauta ga mutum 600 a asibitin ido (Eye Centre) da ke tsohuwar kasuwa a birnin Katsina.
Ya ce gidauniyar ce ta ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya, bayan kammala tantance waɗanda suka amfana, yana mai jaddada cewa ba a karɓar ko sisi daga hannun marasa lafiya.
Alhaji Kabir ya bayyana cewa a wannan zagaye, sama da mutum 2,000 ne za su amfana da ayyukan kula da ido, waɗanda suka haɗa da ba da magunguna, tabarau da kuma tiyatar ido ga masu buƙata.
Ya ƙara da cewa baya ga ayyukan lafiya, gidauniyar na ci gaba da gudanar da wasu shirye-shiryen jin ƙai da ci gaban al’umma a faɗin Jihar Katsina.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da aikin sun bayyana farin cikinsu tare da gode wa Alhaji Dahiru Barau Mangal bisa wannan tallafi na kyauta da ya sauya musu rayuwa.
