Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta sami nasarar daƙile wani yunƙurin satar shanu tare da ƙwato dabbobi 76 da aka sace, waɗanda suka haɗa da shanu 20 da tumaki 56, a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Dutsinma.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ya ce lamarin ya faru bayan da wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari ƙauyukan Yarmaje da Alasawa tare da sace dabbobi da dama.
Sanarwar ta bayyana cewa, bayan samun kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da jami’an rundunar tsaron al’umma ta Jihar Katsina (CWC) sun bi sawun maharan har zuwa yankunan Faguwa da Garangamawa, inda aka yi musayar wuta tsakaninsu da maharan.
Sakamakon matsin lambar da jami’an tsaron suka yi, maharan sun yi watsi da dabbobin da suka sace tare da tserewa, lamarin da ya ba jami’an damar ƙwato dabbobin baki ɗaya.
Haka kuma wata tawagar sintiri ta haɗin gwiwa jami’an tsaro ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci a kauyen Tsintsaye da ke ƙaramar hukumar Musawa.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Babangida Lawal mai shekaru 28 da Ismail Lawal mai shekaru 25. Sai dai mutum na uku da aka gani ɗauke da bindigar AK-47 ya harba bindiga kafin ya tsere daga wurin.
Jami’an tsaron sun samu harsasan bindigar AK-47 guda biyu da aka harba a matsayin hujja, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano inda wanda ya tsere yake da kuma sauran masu hannu a lamarin.
Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar jami’an tsaron da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
