A halin yanzu, babu shakka Arewa na matuƙar buƙatar mafita daga matsalolin rashin tsaro, musamman ta’addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
A cikin wannan makon ne muka samu rahoton yadda wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi garkuwa da wani Alƙalin Babbar Kotu a Jihar Kebbi. Haka kuma, an kuma yi garkuwa da wani ɗan siyasa a Jihar Zamfara. Waɗannan al’amura abin takaici ne matuƙa.
Sai dai, a wani ɓangaren kuma, an kama wasu da ake zargi da hannu wajen sace ɗalibai a Jihar Oyo, inda ake cewa alamu sun nuna yawancinsu ‘yan Arewa ne. Wannan na ƙara fito da cewa matsalar tsaron Arewa ba ta rasa alaƙa da wasu daga cikin ‘ya’yanta.
Tun a lokacin gwamnatin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, Nijeriya ta fuskanci manyan matsalolin tsaro. A wancan lokaci ne aka yi garkuwa da ɗaliban makarantar Chibok a Jihar Borno, tare da yawaitar hare-haren bama-bamai.
Bayan haka, gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta yi ƙoƙari wajen daƙile ayyukan Boko Haram. Duk da haka, a ƙarshen mulkinsa sai aka samu ƙaruwar matsalar garkuwa da mutane da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
A yanzu kuma, a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, an sake fuskantar barazanar wasu ƙungiyoyi irin su Lakurawa. Don haka, idan har za mu yi adalci, dole ne mu fara gano tushen matsalar kafin mu yanke hukunci.
Gaskiya ne ana iya samun masu ra’ayin cewa ya kamata a sauya gwamnati, amma siyasa tana tafiya ne da lissafi. Yawancin gwamnonin Kudu na tare da Shugaba Tinubu, haka kuma da dama daga cikin gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC ne. Saboda haka, sauya irin wannan gwamnati ba abu ne mai sauƙi ba.
A gefe guda kuma, dole ne ‘yan adawa su kawar da son rai, ƙyashi da rarrabuwar kawuna idan suna son su zama madadin gwamnati mai ƙarfi.
A matsayina na mai nazari, ina ganin lokaci ya yi da za mu fara gyara kanmu, mu haɗa kai, sannan mu yawaita addu’ar Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar rashin tsaro tare da ba Nijeriya zaman lafiya mai ɗorewa.
Daga: Mukhtar Ibrahim Sa’ullawa, Katsina. 07066434519/08080140820.
