An zargi sojoji da harbin ɗan kasuwa yayin sintiri a Mubin Adamawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma a garin Mubi na Jihar Adamawa sun shiga alhini bayan zargin jami’in soja da harbin wani ɗan kasuwa mai suna Suleiman Abi, a lokacin da suke gudanar da aikin sintiri a Ƙaramar Hukumar Mubi ta Arewa.

Al’amarin ya auku ne da misalin 8:40 na ranar Lahadi, wanda ya haifar da alla-wadai da gudanar da zanga-zangar lumana daga ‘yan yankin kan kira na a tabbatar da gaskiya da adalci a kai.

A cewar mazauna, al’amarin ya faru ne a lokacin da mutumin yake tuƙa babur ɗinsa na laturoni, inda ya gano cewa sojojin suna gudanar da sintiri. Kasancewar ya tsorata da kame saboda dokar taƙaice zirga-zirgar babura daga ƙarfe 9 na dare zuwa 6 na safe, sai ya juya da nufin tafiya gida kafin dokar ta fara aiki.

Wani shaida ya yi zargin wani soja ne ya bi Abu tare da buɗe masa wuta a lokacin da yake ƙoƙarin rufe ƙofar shiga gidansa bayan ya ajiye babur ɗin nasa.

Ya bayyana cewa, alburushin ya kuskure shi ne a kafa da fari kana ya kuma samu haɓarsa, lamarin ya bar shi cikin jini sakamakon raunukan harbin.

Akan haka ne maƙota suka garzaya tare da kama sojan, saidai daga bisani sun sake shi bayan shiga tsakani da manyansa da jagororin al’umma suka yi.

Da fari an garzaya da Suleiman Abu ne Babban Asibitin Tarayya da ke Mubi, sannan daga bisani aka sauya masa da Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, inda a nan yake karɓar kulawa a halin yanzu.

By Babaji

Leave a Reply