
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai fara hutun mako biyu daga ranar Alhamis, 6 ga watan Agusta, 2026 bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince masa, lamarin da ke nuna karon farko da irin haka ya faru tun bayan hawansu kan karagar mulki a shekarar 2023.
Wannan hutu zai ba wa mataimakin shugaban ƙasar damar yin amfani da lokacin wajen yin nazari da kuma sararawa domin sabunta karsashinsa na cigaba da hidimta wa ƙasa da kuma kimtsa wa shirye-shiryen zango na gaba na gwamnatin nasu.
Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce hutun zai ba wa Sanata Shettima damar yin nazari kan shirye-shiryen da gwamnatin take aiwatarwa da zurfafa fahimtarsa kan tsare-tsaren ƙasa da na ƙasa-da-ƙasa da kuma ƙara bayar da himma wajen faɗaɗa hanyoyin aiwatar da shirin Sabunta Fata na shugaban ƙasa.
A cewar sanarwar, Shettima ya kasance cikin ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa, sanya ido akan dabarun samar da shirye-shiryen gwamnati musamman akan fannonin ci-gaban harkar tattali, tsaron abinci, ayyukan jin-ƙai, amfani da sadarwar zamani ta dijital, samar da ayyukan yi da kuma haɗin kan shiyyoyi yayin mulkin nasu.
Ta ƙara da cewa, Sanata Shettima zai cigaba da kasancewa mai kiyaye ƙa’idojin biyayya, aiki da hidimar al’umma da kuma taka muhimmiyar rawa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
