
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta damƙa rahotonta na wucin-gadi ga Shugaba Bola Tinubu kan binciken da ta gudanar akan badaƙalar ƙagaggiyar hukumar nan ta bogi (PFIPC), inda ta bayar da shawarar a gurfanar da wanda aka zarga cewa shi ne Darakta-Janar, Adeniyi Adeyemi.
Shugaban ICPC, Musa Aliyu ya bayyana haka a ranar Alhamis bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kwana 30 da shugaban ya umarci hukumar yaƙi da rashawan da ta gudanar da cikakken bincike akan zargin badaƙalar PFIPC.
A cewar Aliyu, binciken ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ba a taɓa naɗa Adeyemi ba, sannan takardun da aka gabatar da su a matsayin na naɗin da wasu harkokin PFIPC na bogi ne.
Aliyu ya kuma ce binciken nasu ya gano cewa an samu gazawa daga ɓangaren tantancewar gwamnati da hanyoyin sanya ido, wanda ya bayar da damar ɗaukar PFIPC a matsayin halastacciyar cibiyar gwamnati.
A cewarsa, masu binciken nasu sun kuma gano cewa ana zargin Adeyemi da kafa wasu hukumomi biyu – wato Hukumar Ciyar da Harkokin Zuba Jari ta Abuja (FIFA) da Hukumar Haɗakar Masu Zuba Jari na Ƙasashen Waje da na Masu Haɗaka (PIPA-PPP).
Ya ƙara da cewa, hukumar ta shawarci a gurfanar da Adeyemi, a hukunta jami’an gwamnatin da aka zargi sakacinsu da taimaka wa wanzuwar hukumar bogin da kuma yin wasu gyare-gyare da nufin ƙarfafa harkokin gudanarwar cikin gida na ma’aikatu, rassa da hukumomin gwamnati.
Kazalika, ya ce rahoton da suka miƙa wa shugaban ƙasar na wucin-gadi ne, yayin da ake cigaba da bincike domin gano sauran abokan hulɗa a cikin batun da kuma ƙarfafa shari’a a kai.
