Kamfanin barasa a Nijeriya ya samu ribar Naira biliyan 164 cikin wata shida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin barasa na Nigerian Breweries ya sanar da samun ƙarin kuɗaɗen shiga da kashi tara cikin ɗari a tsakiyar shekarar 2026, inda ya samu Naira biliyan 804, yayin da ribar aikinsa ta kai Naira biliyan 164, alamar ci gaba da farfaɗowar harkokin kuɗinsa.

Sakamakon kuɗaɗen da kamfanin ya fitar na watanni shida da suka ƙare a ranar 30 ga Yuni, 2026, ya nuna cewa kuɗaɗen shigar sun ƙaru daga Naira biliyan 738 da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar 2025.

Kamfanin ya kuma samu ƙarin ribar aiki da kashi takwas cikin ɗari, inda ta tashi daga Naira biliyan 152 zuwa Naira biliyan 164, duk da cewa kuɗaɗen talla, rarrabawa da gudanarwa sun ƙaru da kashi 20 cikin ɗari.

Rahoton ya nuna cewa raguwar kuɗaɗen da kamfanin ke kashewa wajen biyan kuɗaɗen lamuni da sauran nauyin kuɗi ta taimaka wajen ƙara ribar kafin haraji da kashi 18 cikin ɗari.

Sai dai kamfanin ya ce fara aiwatar da sabon tsarin haraji ya rage saurin haɓakar ribar bayan haraji, wadda ta ƙaru da kashi biyar cikin ɗari kacal.

A cikin wata sanarwa, Sakataren Kamfanin kuma Daraktan Harkokin Shari’a, Uaboi Agbebaku, ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga ingantaccen tsarin sarrafa kuɗaɗen shiga, ci gaba da saka hannun jari a manyan nau’ikan kayayyakin kamfanin, da kuma bunaasar kasuwancin nau’ikan barasa masu inganci da na malt.

Ya ce duk da ƙalubalen tattalin arzikin ƙasar, kamfanin ya ci gaba da nuna juriya tare da samun ci gaba.

A cewarsa, ƙarin kuɗaɗen shiga ya samo asali ne daga kyakkyawan tsarin gudanar da kasuwanci, saka hannun jari a manyan kayayyaki, inganta ayyuka a dukkan matakan samar da kayayyaki, da kuma gudunmawar da manyan nau’ikan barasa da kayayyakin malt suka bayar.

By ukarofi