Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gidauniyar Dahiru Bara’u Mangal ta fara aikin tantance marasa lafiyar da suka samu wannan dama, inda ake gudanar da gwaje-gwaje domin gano irin matsalar da kowanne mara lafiya ke fama da ita da kuma tantance waɗanda suke buƙatar aikin tiyata ko magani.
Sama da mutane 120 ne ake sa ran za su amfana da aikin, wanda za a gudanar da shi kyauta ba tare da marasa lafiyar sun biya kuɗin magani ko aikin tiyata ba.
Da yake bayyana yadda shirin yake, ɗaya daga cikin ’yan Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Hussaini Kabir, ya bayyana cewa tun bayan fara irin wannan tallafi, sama da mutum 2,000 ne suka samu damar amfana da aikin gyaran lalurar fitsari da sauran tallafin lafiya da gidauniyar ke bayarwa.
Ya ce gidauniyar ta ɗauki nauyin gudanar da aikin ne domin rage wa marasa lafiya da iyalansu wahalar da suke fuskanta, musamman waɗanda ba su da halin biyan kuɗin aikin tiyata da magunguna.
Hussaini Kabir ya ƙara da cewa ana fara aikin ne da tantance marasa lafiyar, kafin a gudanar da gwaje-gwajen da suka dace domin tabbatar da matsalar da suke fama da ita. Bayan haka ne ƙwararrun likitoci za su tantance waɗanda suke buƙatar tiyata ko kuma magani.
