INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓen gwamnan Osun a shafinta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da fara ɗora sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun a shafinta na yanar gizo na IReV, inda tuni aka riga aka ɗora na mazaɓu guda 402 daga cikin 3,763 zuwa ƙarfe 4:03 na yammacin Asabar.

Wannan adadi ya wakilci kaso 10.68 na jimillar mazaɓun ƙananan hukumomi 30 na faɗin jihar. An fara aikin ne bayan kammala zaɓe da fara tantancewa da ƙirgawa a mazaɓun sassan Osun.

Shafin na IReV na bayar da dama ga al’umma, jam’iyyun siyasa, masu sanya ido da sauran masu ruwa da tsaki su yi nazari akan sakamako bayan jami’an zaɓe sun ɗora.

INEC ta samar da tsarin ne da nufin ƙarfafa tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da harkokin tattara sakamakon zaɓe, wanda a baya ma ta yi amfani da shi a zaɓuka daban-daban har da na gwamna.

Da fari, Mawaƙi David Adelda aka fi sani da Davido ya koka kan yadda aka samu jinkiri wajen ɗora sakamakon zaɓen inda ya ƙalubalanci dalilin hakan, yana mai kira ga INEC da ta tabbatar da gaskiya da adalci yayin hakan.

Hakan na zuwa ne bayan an kammala kaɗa ƙuri’a a mazaɓu da dama, inda yake tambayar mai ya sa har zuwa lokacin ba a fara ganin sakamako a shafin IReV ba.

Daga bisani a ƙarfe 4:36 na yammacin rahotanni sun nuna cewa an ɗora na jimillar mazaɓu 753, wato wanda ke wakiltar kaso 19.53.

By Babaji