Sabon harin Sakkwato ya yi ajalin mutane bakwai da sace 17 a ƙauyuka uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ƙauyuka guda uku farmaki a Ƙaramar Hukumar Wurno da ke Jihar Sakkwato, inda suka halaka mutum bakwai da kuma sace wasu guda 17 da suka haɗa da mata 15.

Ƙauyukan da aka afka wa sune Dinawa, Munƙi da Gidan Dare, inda maharan suka ɗauki tsawon sa’o’i suna atisaye a daren Litinin, bayan amfani da damar mamakon ruwan sama da aka zabga a yankin.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban ‘yan bijilante na yankin Dinawa, Aliyu Falke, ya ce an yi jigilar maharan ne a wata tirela da misalin ƙarfe 10:30 na dare. A cewarsa, sun gano haka ne bayan ajiye motar a wani guri da ke kusa da yankin.

Ya ce, bayan mintina 15 da haka ne ‘yan bindiga suka fara ƙaddamar da harbe-harbe, inda a nan take suka halaka mutum biyu ciki har da ɗaya daga cikin mutanensa mai suna Sani Wukari.

Ya bayyana cewa, ganin haka ya sa ‘yan bijilanten suka mayar da martani wajen yin musayar wuta da su, saidai ƙarfin makaman ‘yan bindigar ya sa suka ja da baya, lamarin da ya sa suka shiga garin suka gudanar da farmakin nasu.

Sannan, an halaka wasu mutane biyar ciki har da mata biyu. Sannan sun raunata mutane huɗu har da Falke da yin awon-gaba da mata shida da wani mutum, kamar yadda jagoran ‘yan bijilanten ya bayyana.

Ya ƙara da cewa, ‘yan sanda sun kai ɗauki daga bisani tare da yin arangama da su, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa daga yankin.

Waɗanda aka halaka a harin Dinawa sun haɗa da Malami Dogo, Chairman Maidawa, Altine Mesi, Alhaji Shua’ibu, Balaraba Abdullahi, Hafsatu Salisu da kuma Sani Wukari. Sai waɗanda suka jikkata, Abdullahi Maikano, Garba Nabuga da kuma Anas Abubakar, idna tuni aka garzaya da su asibiti domin ba su kulawa.

By Babaji

Leave a Reply