Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan bindiga sun farmaki ayarin motocin Gwamnan Osun yayin da jami’an tsaro suka daƙile harin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba wasu ‘yan bindiga suka farmaki tawagar motocin da ke yi wa Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun rakiya, jim-kaɗan bayan kai ziyara a fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaron gwamnan.

Rahotanni sun bayyana cewa, ba-takashin, wanda aka shafe tsawon mintina 12 zuwa 15, ya faru ne bayan gwamnan ya fice daga fadar basaraken, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici.

Gwamnan ya isa fadar mai martaban ne da misalin ƙarfe 3:15 na rana a wani ayarin motoci guda 20 bayan barin hedikwatar hukumar zaɓe ta ƙasa da ke Osogbo, inda ya je karɓo shaidar zama gwamna bayan sake lashe zaɓe a ƙarshen makon da ya gabata.

Wata shaida da ta gana da manema labarai, ta ce an fara jin hayaniya ne bayan sarkin ya yi wa gwamnan addu’o’i a lokacin da ya gabatar masa da shaidar sake cin zaɓen nasa. A cewarta, Adeleke ya fice daga ɗakin ganawar ta wata ƙofa da aka ajiye wa sarki da iyalansa a lokacin da aka fara harbe-harben.

Wata ƙaramar ‘yar kasuwa mai suna Munirat ta ce, ta yiwu maharan suna da masaniya kan ziyarar gwamnan don haka suka jira zuwansa. Ta bayyana cewa, bayan sun je wajen a wata mota ƙirar Sienna, sun shiga ta ainihin ƙofar fadar, inda suka fara harbe-harbe, amma jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin mayar da martani cikin hanzari, lamarin da ya tilasta musu ja da baya.

Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Kolapo Alimi ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce jami’an tsaron da ke tare da gwamnan sun yi nasarar daƙile harin, kuma babu wanda aka halaka ko raunata.

By Babaji

Leave a Reply