Yanzu-yanzu: Tinubu ya maye gurbin Didi Walson-Jack da Abel Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Abel Enita a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, wanda zai fara a ranar 27 ga Agusta, 2026.

Hakan na nufin Enitan zai maye gurbin Misis Didi Walson-Jack a muƙamin, wadda a kwanan nan za ta yi ritaya bayan cika shekaru 60, kamar yadda doka ta tsara.

Enitan, wanda ɗan ainihin Jihar Osun ne, shi ne mafi girma kuma Babban Sakatare da Ma’aikatar Ma’aikatan Tarayya, wanda yake da ƙwarewa a harkar gudanarwa da kuma fahimtarsa ga ayyukan sabon nauyin da aka ɗora masa.

Ya kasance a matsayin babban sakatare har na tsawon shekara bakwai da wata bakwai, wanda a yayin haka ya yi aiki da Ma’aikatar Harkokin ‘Yan sanda, Ma’aikatar Jin-ƙai da kuma Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. A yanzu shi ne Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Yayin da Shugaba Tinubu ke sanar da matakin, ya miƙa godiyarsa ga Walson-Jack bisa ƙoƙarinta da gudumawa da ta bayar wajen hidimta wa ƙasa da kuma gyare-gyare, tasiri da ƙirƙire-ƙirƙire da aka samu a ƙarƙashin jagorancinta, yana mai mata fatan alheri da gamawa lafiya yayin da ta yi ritayar.

Haka kuma, ya yi kira ga sabon shugaban da ya ɗora daga inda ta tsaya wajen tabbatar da cimma nasarori a harkokin gudanarwar ma’aikatar tare da tabbatar da tsare gaskiya da adalci domin amfanin ma’aikatar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply