Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya umarci kame yayin da aka gano hukumar bogi a ofishin sakataren gwamnati

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta kama Frins George Buchi Nwabueze bisa zargin sa da alaƙa da ofishin da aka gano na “National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office”.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ce ta gano hukumar bogin a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume. Shugaban ICPC Dakta Musa Adamu Aliyu (SAN) ne ya bayyana haka yayin ganawa da wakilan Fadar Shugaban Ƙasa jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaban Ƙasar a yau Juma’a.

Adamu ya ce, an gano sabuwar hukumar bogin ne yayin da ake bincike kan hukumar bogi ta Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda Adeyemi Matthew ya gudanar.

Ya bayyana cewa, sun gano an bai wa hukumar ofishi ta haramtacciyar hanya a farfajiyar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya OSGF.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya umarci a gaggauta dakatar da manyan sakatarori uku: M.S. Danjuma, Injiniya Nadungu Gagare da kuma Richard P. Pheelangwah kan al’amarin.

Ana cigaba da tattara bayanai…

By Babaji

Leave a Reply