Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Kwamitin Duba Barazanar Tsaron ƙasa (National Threat Assessment) da kuma Tsarin Ayyukan Tsaron ƙasa na Shekaru biyar, domin inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, leƙen asiri da rundunonin sojin Nijeriya.
Shugaban ya kuma naɗa Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa, a matsayin wanda zai jagoranci aikin tare da samar da sakatariyar kwamitin mutum 11 da aka kafa domin tsara sabon tsarin tsaron ƙasar.
An bayar da umarnin ne ranar Laraba yayin taron Majalisar Zartarwa ta ƙasa (FEC) da aka gudanar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, kwamitin ya ƙunshi mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle; Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu; Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; da Babban Hafsan Ruwa, Vice Admiral Idi Abbas.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta ƙasa (DSS), Tosin Ajayi, da Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta ƙasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed.
Shugaba Tinubu ya ce manufar sabon tsarin ita ce samar da tsari guda ɗaya na ƙasa wajen gano barazanar tsaro, tsara abubuwan da ya kamata a ba fifiko da kuma daidaita ƙarfin hukumomin tsaro da sabbin yanayin barazanar da ƙasar ke fuskanta.
Ya bayyana cewa tantancewar barazanar tsaro zai samar da cikakken fahimta kan yanayin tsaron ƙasar ta hanyar gano manyan barazanar da ake fuskanta, tantance muhimmancinsu da kuma tsara manufofin da za su jagoranci ayyukan tsaro.
Shugaban ya ce tsarin ayyukan tsaro na shekaru biyar zai mayar da wannan tantancewa zuwa manufofin aiki na zahiri, tare da bayyana irin rundunonin da ake buƙata a wuraren da ake gudanar da ayyukan tsaro daban-daban, gano gibin kayan aiki da ƙarfin aiki, bukatun kayan yaƙi da dabarun sufuri, da kuma tsara lokacin aiwatar da shirin.
Tinubu ya ce duk da nasarorin da aka samu a wasu ayyukan tsaro a baya-bayan nan, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci.
Ya kawo misali da aikin da hukumomin tsaro suka gudanar wajen ceto ɗalibai da malamansu da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, yana mai cewa aikin ya nuna irin abin da hukumomin tsaro za su iya cimma idan suka yi aiki tare bisa sahihin bayanan leƙen asiri da manufa guda.
Shugaban ya kuma ce a baya wasu ayyukan tsaro ana tsara su ne daban-daban daga kowace hukuma, ba tare da dogaro da wani cikakken tsarin tantance barazanar tsaro na ƙasa ko matsakaicin tsarin aiki na shekaru ba. Ya ce hakan na rage ingancin haɗin gwiwa da kuma yadda ake amfani da albarkatun ƙasa.
Tinubu ya umarci kwamitin da ya fara aiki nan take, tare da miƙa cikakken rahoton Tantance Barazanar Tsaro ta ƙasa da Tsarin Ayyukan Tsaron ƙasa na Shekaru Biyar cikin kwanaki 90 domin shugaban ya duba kuma ya amince da shi.
Ya kuma ba kwamitin damar tuntuɓar ko kuma haɗa wakilan ma’aikatu, hukumomi da sauran sassan gwamnati da abin ya shafa idan buƙatar hakan ta taso, domin tabbatar da cewa tsarin ya shafi dukkan fannoni masu muhimmanci na tsaron ƙasa.
Da zarar an amince da shi, tsarin ayyukan tsaron na shekaru biyar zai zama babban tsarin da zai jagoranci ayyukan soji da tsaron Nijeriya na matsakaicin lokaci.
Haka kuma, tsarin zai zama tushen tsara kashe kuɗaɗen tsaro da sayen kayan aiki na shekaru masu zuwa, domin tabbatar da cewa kasafin kuɗin gwamnati ya dace da abubuwan da aka bai wa fifiko wajen tsaron ƙasa.
Shugaban ƙasa ya kuma umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya da Ofishin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaron ƙasa da su ɗauki duk matakan da suka dace domin fara aiwatar da umarnin nan take.
