Yaƙin neman zaɓen APC: Ƙungiyar Arewa ta jinjina wa Tinubu kan saka Yerima Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Arewa Community APC a jihohin kudanci 17, ta taya Alhaji Kwamared Yerima Shettima kan samun muƙamin Darakta na Hulɗar Ƙwadago na II a kwamitin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC a zaɓukan 2027.

Da yake magana a Gusau, Jihar Zamfara a ranar Lahadi Frins Alhaji Aliyu Bambado na II, wanda shi ne Galadiman Legas na I kuma mai bayar da shawara ga ƙungiyar Community APC a Legas da jihohin kudu 17, ya bayyana naɗin Shettima a matsayin ajiye ƙwarya a gurbinta duba da yadda yake da ƙwarewa da jajircewa a harkar shugabanci.

Ya bayyana cewa, muryar Shettima a fagen siyasar Arewa ta shahara musamman wajen zama jagora a ƙungiyar Arewa Youth Consultative Forum AYCF, Northern Stakeholders Consultative Initiative NSCI, kuma mamba a ƙungiyar Fasto Tunde Bakare’s ta Save Nigeria Group, sannan mai ruwa da tsaki a NADECO tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewarta, Shettima ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen harkokin ci-gaban al’umma, warware rikici da wayar da kan jama’a kan siyasa a Legas da sassan shiyyar Kudu maso Yamma. Haka ma kasantuwarsa mataimakin shugaban jam’iyyar Young Democrats Party YDP gami da ƙoƙarinsa a hidimar al’umma.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi masa addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa bisa gaskiya da adalci yayin neman sake zaɓar Shugaba Tinubu da Sanata Kashim Shettima a 2027.

By Babaji

Leave a Reply