2027: Tinubu ya janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci a janye tare da sake tsara jaddawalin ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓensa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC domin babban zaɓen 2027. Umarnin ya biyo bayan cece-kuce akan jaddawalin da aka fitar da fari a ranar Asabar.

A cewar jaridar TheWill, Tinubu ya ɗauki matakin ne bayan ƙorafi daga wasu jiga-jigan ‘ya’yan APC da suka ce jaddawalin bai ƙunshi wasu muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ba kuma bai yi daidai da tsarin shugabanci da rarrabawa da kuma tsarin jam’iyyar ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa, Tinubu ya umarci Fadar Shugaban Ƙasa, jagorancin Majalisar Dokokin Ƙasa da Kwamitin kula da Harkokin APC (NWC) da su janye takardar farkon tare da yin nazari a kai da kuma warware wuraren da ake da damuwa akansu tare da fitar da sabon jaddawali.

A cewar majiyoyin, Tinubu bai ji daɗin gano wasu kurakurai acikin jaddawalin farkon ba musamman ganin cewa tsarin yaƙin neman zaɓen shi ne ke da ikon haɗa kan masu ruwa da tsaki da jiga-jigan ‘ya’yan APC gabanin zaɓen 2027.

Wata majiya ta ce: ” Shugaban ya yi mamakin ganin ƙalilan daga cikin jiga-jigai kuma masu ƙwarewa a jam’iyyar a jaddawalin yaƙin neman zaɓen nasa da aka fitar.”

Jaddawalin dai ya nuna cewa, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ne Darakta-Janar na yaƙin zaɓen Tinubu. Amma daga bisani, an koka kan rashin ganin sunayen wasu jiga-jigan APC da dama aciki, waɗanda ana ɗaukarsu a matsayin jinshiƙan siyasa a jihohi da shiyyoyinsu. Daga cikin abin da ya janyo haka, akwai rashin ganin sunan mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.

A ƙarƙashin jaddawalin farkon Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio shi ne wanda aka saka a matsayin mataimakin darakta janar na yaƙin neman zaɓen kudanci, tare da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni. Yayin da Jagora a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril su kuma a matsayin kodentoci.

Rahoton ya nuna cewa, masu ruwa tsakin sun koka akan yadda shugaban majalisar dattawa ya samu muƙami na ƙasa da wasu waɗanda su ma ‘ya’yan majalisa ne acikin jaddawalin, wanda hakan ya saɓa wa tsarin shugabanci a dokance.

By Babaji

Leave a Reply