Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan bindiga sun kashe mutane biyar a ƙaramar hukumar Dutsinma ta Jihar Katsina.
A hira da wata kafar sadarwa na JBC ta yi da mazaunin garin Dutsinma, ‘yan bindigan sun shiga garin Karofi inda suka kashe wani matashi mai suna zaharaddeen,suka jikkata wasu tare da kwashe Dabbobi.
Haka kuma sun shiga ƙauyen Dage Lawal nan ma suka kashe mutane uku ciki har da wani tsohon Kansila da ɗan sa.
Mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunnan sa, ya bayana cewa mutanen garurruwan sun nemi ɗauki daga jami’an tsaro na karamar hukumar amma saboda rashin kayan aiki sun kasa isa ƙauyukan.
Ya ce mota mai Sulke (APC) ɗaya ce jami’an tsaron ne gare su, gashi ƙananan mota basa shiga ƙauyukan.
Ya ƙara da cewa tun kafin kai hare haren sun taru a garin Makeri ,sai da duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro su ka yi a yankin ba su iya tunkarar ‘yan bindigan ba saboda basu da isassun kayan aiki.
A halin yanzu al’ummar ƙaramar hukumar Dutsinma sun shiga fargaba domin kullun ‘yan bindiga sai sun shiga ƙaramar hukumar a cewar mazaunin yankin.
Ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan bindiga da suke kai hare hare a ƙaramar hukumar waɗanda aka yi sulhu da su ne suke aikata ta’addancin domin ana ganin fuskokinsu.
Ya yi kira ga mahukunta da su ɗauki mataki na gaggawa na basani ba sabo domin a halin yanzu manoma a wasu ƙauyen basa iya zuwa gonakin su.
