Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ƙungiyar haɗin kan al’ummar ƙabilar Agatu ta jihar Nasarawa don Wadada wato Agatu United For Wadada a turance ta kammala shirye-shiryen ƙaddamar da wata ƙungiyar yaƙin neman zaɓen ta domin goyon bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress APC a babban zaɓen 2027 wato sanata Ahmed Aliyu Wadada.
Kodinetan ƙungiyar a jihar kwamaret Godspower Ede ne ya bayyana haka a cikin wata hira ta musamman da ya yi da wakilin mu a Lafiya ranar Litinin na makon da ake ciki.
Ede yace taron ƙaddamarwar da aka tsara za a yi a ƙarshen wannan mako wato ranar Asabar 29 ga watan Augusta da shekarar 2026 da ake ciki mai taken: “ƙarfafa ‘yan uwantaka da haɗin kai don cigaban ƙasar Agatu da jihar Nasarawa” wato Strenthening Brotherhood And Unity For The Development Of Agatu Nation and Nasarawa State a turance na da nufin ƙarfafa tara jama’a musamman a matakin jihar da yankunan karkara da kuma nuna goyon baya ga ɗan takarar APC ɗin a faɗin jihar gabanin zaɓen.
A cewarsa taron zai haɗa da ƙaddamar da jami’an yaƙin neman zaɓen Wadada ɗin na musamman da aka zaɓa daga cikin al’ummar Agatu da saƙon barka da ƙwarin gwiwa daga wasu manyan baƙi da suka haɗa da mataimakin gwamnan jihar Dakta Emmanuel Akabe da shugaban jam’iyyar APC a jihar Dakta Aliyu Bello da sabon nadadden kwamishinan jihar Dakta Nawani Aboki da ɗan majalisar dokokin jihar Musa Ibrahim Abubakar da sauran su inda za su kuma gabatar da ƙudurin da zai tabbatar da nasarar Sanata Aliyu Wadada a zaɓen.
Kodinetan tafiyar kwamaret God’spower Ede ya kuma bayyana Sanata Wadada a matsayin mafi cancanta a cikin dukkan ‘yan takaran bisa tarihin sa na taimakon ‘yan Adam da tallafawa marasa ƙarfi ba tare da nuna banbancin siyasa da addini ko ƙabila ba.
Ede ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira ga sauran ƙabilu da ƙungiyoyin al’adu a jihar da su yi koyi da wannan yunkuri ta hanyar kafa tsari da zai tara ‘yan uwan su domin zaɓen dan takarar APC ɗin domin tabbatar da miƙa mulki cikin lumana daga gwamnatin gwamna Abdullahi Sule zuwa ga shi Wadada.
A ƙarshe sai ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa da haɗin kai da aiki tare tabbas ba shakka Sanata Ahmed Aliyu Wadada zai zama zakara cikin duka ‘yan takaran bayan zaɓen gwamnan na 2027.
