Gwamna Sule ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas da sakatarori shida

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas a matsayin mambobin majalisar zartarwar jihar.

Gwamnan ya kuma rantsar da sabbin sakatarori na dindindin kuda shida da sabbin masu bashi shawarwari na musamman guda 11 da wani mamba na hukumar kula da ayyukan shari’a ta jihar da kuma wani mamba na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar da akafi sani da NASIEC duk a yau Laraba 26 ga watan Augusta na shekarar 2026 da ake ciki a Lafiya babban birnin jihar.

A taron rantsarwar gwamna Sule ya buƙaci su rungumi manufofi da shirye-shiryen gwamnatin sa domin cigaba da kawo cigaba masu ma’ana a faɗin jihar.

Ya kuma buƙaci sabbin kwamishinonin da masu ba shi shawara sakatarorin da sauran su da su mayar da hankali waje guda su kuma gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son kai ko tsoro ba.

Sabbin wadanda aka rantsar wakilin mu a jihar ya rawaito cewa sun haɗa da:

  1. Nawani Aboki- Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu da yawon buɗe ido
  2. Ashefo Paul – Kwamishinan binciken ƙasa da tsare-tsaren birane
  3. Baba Shehu- Kwamishinan ƙungiyoyi masu zaman kansu
  4. Ahmed Yakubu – Kwamishinan ƙasa da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar.
  5. Jibril Ibrahim – Kwamishinan matasa da wasanni.
  6. Mohammed Oyigye- Kwamishinan noma da tsaron abinci
  7. Muhammad Habeeb-Nagogo – Kwamishinan Ilimin manyan makarantu da fasaha.
  8. Rebecca Kpadji – Kwamishiniyar harkokin mata da cigaban jama’a.

Gwamna Sule ya buƙace su da su rungumi manufofin gwamnatin sa da aka gina bisa lissafi da gaskiya da kuma kula da albarkatun gwamnati cikin hikima.

Yace ya sake tsara majalisar sa ne domin ƙarfafa mulki da kuma ƙara inganta rayuwar mutanen jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa an zaɓi sabbin sakatarori na dindindin ne bisa cancanta da kuma tsarin bai ɗaya.

Ya gode wa shugaban majalisar dokokin jihar Danladi Jatau da sauran ‘yan majalisa bisa tantancewa da tabbatar da waɗanda aka naɗa cikin lokacin da kuma haɗin kai wajen bunƙasa jihar.

Tun farko a jawabinsa sakataren gwamnatin jihar ta Nasarawa Labaran Magaji yace an yi naɗin ne domin ƙarfafa mulki da bunƙasa cigaba a jihar.
Ya tabbatar wa gwamnan cewa waɗanda aka naɗa za su ba shi cikakken goyon baya da biyayya.

Da yake jawabi a madadin sabbin kwamishinonin kwamishinan yaɗa labarai da al’adu da yawon buɗe ido Nawani Aboki ya gode wa gwamnan bisa ganin su sun cancanci naɗin.
Yayi alƙawarin cewa za su mayar da hankali su kuma gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son kai ko tsoro ba kamar yadda gwamnan ke buƙata.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamna jihar Dr. Emmanuel Akabe da shugaban majalisar jihar Danladi Jatau da na Mai martaba sarkin Lafiya Alh. Justice Sidi Bage mai ritaya da mai shari’a Aisha Bashir-Aliyu da babbar alƙaliyar jihar da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Dr. Aliyu Bello da sauran manyan baƙi.

By ukarofi

Leave a Reply