Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, na daga cikin ɗimbin jama’a da suka halarci hawan Gani da aka gudanar a Masarautar Daura. Wani gagarumin biki na gargajiya da ake gudanarwa duk shekara a matsayin wani ɓangare na bukukuwan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Hawan Gani na daga cikin muhimman al’adun Masarautar Daura, inda sarakuna, hakimai, dagatai, masu unguwanni da sauran al’umma ke fitowa cikin ƙayatattun kayan gargajiya domin nuna al’adun masarautar tare da yin murnar wannan rana mai albarka.
Haka kuma makaɗa da mawaƙan gargajiya,wasan Kokawa da damben gargajiya na da cikin wasanni da a kan gudanar a wajen hawan Gani.
Bayan kammala hawan, Gwamna Raɗɗa ya taya ɗaukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), tare da addu’ar Allah ya ci gaba da ba al’ummar musulmi zaman lafiya da albarka.
Gwamnan ya kuma jinjinawa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, bisa irin ƙoƙarin da yake wajen karewa da raya al’adun gargajiya na Masarautar Daura, yana mai addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya, ƙarfi da hikimar jagoranci.
Haka nan, Gwamna Raɗɗa ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa ba jihohi dama da goyon baya wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma.
A ƙarshe, Gwamna Raɗɗa ya roƙi al’ummar Katsina da ƙasa baki ɗaya da su ci gaba da sanya jihar da ƙasar nan cikin addu’o’insu, domin samun zaman lafiya, ci gaba da wadata.
Sauran wanda suka halarci taron akwai Ministar Al’adu Barista Hannatu Musawa, Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasir Yahaya Daura, Ƴar Shugaban ƙasa Mujidat Folashade Iyaloja TinubuShugaban ma’aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Sakataren gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin Masarautu Hon. Usman Abba Jaye, da Sauran su.
