Jam’iyyar ADC ta ƙaddamar da jagororin yaƙin neman zaɓe a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirin ta na tinkarar babban zaɓen game-gari na shekarar 2027, ranar Laraba ɗin nan jam’iyyar ADC a jihar Kebbi ta ƙaddamar da jagororin yaƙin neman zaɓe.

Da ya ke jawabi a wajen taron, ɗan takarar kujerar mataimakin gwamna Dakta Musa Zagi Argungu ya bayyana cewa, sanin kowa ne ya’yan jam’iyyar ADC mutane ne da suka san ya kamata, masu bin doka da oda da son zaman lafiya, saboda haka ne ta ke bin ƙa’idojin da dokokin ƙasa da na zaɓe suka gindaya saboda haka ana fatar za su cigaba da bin doka da oda kamar yadda aka san su.

Kamar yadda kuka sani, tuni an riga an ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa, na gwamnoni kuma in sha Allahu za a ƙaddamar da shi nan gaba kaɗan, saboda haka ne aka kaddamar da shugabannin yaƙin neman zaɓe na jiha a ƙarkashin Alhaji Sani Tadurga tare da mataimakan sa daga gundumomin Sanatoci uku da ke akwai a wannan jihar.

An danƙa wannan amanar ne hannun su saboda cancantar su da kuma kyakykyawan zaton za a sami nasara.
Maganar gaskiya akwai alamun nasara saboda tun inda muka fito duk garin da muka biyo sai mun iske cincirindon mutane suna jiran mu duk da ya ke ba wani gangami da muka yi don haka yanzu kowa ya koma mazabar sa a cigaba da neman jama’a ta hanyar wayar musu da kai ba tare da zage-zage ko kage-kagen karya ba kan halin da ƙasar nan musamman wannan yankin na Arewa ya sami kan sa na rashin tsaro talauci da yunwa da aka ƙaƙaba muna.

By ukarofi

Leave a Reply