Zargin sace kayan asibiti: Hukumar NHMB ta kafa kwamitin bincike

Spread the love

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Hukumar kula da asibitoci ta jihar Nasarawa (NHMB) ta kafa wani kwamiti domin binciken zargin sace kayayyakin asibitin gwamnati na yankin rayawa na Umaisha dake ƙaramar hukumar Toto a jihar.

Bincike a kan lamarin ya tabbatar cewa ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazaɓar Ugya/Umaisha Hon. Ibrahim Sa’ad ne ya bai wa asibitin kayan tallafin don a turo su zuwa Umaisha ɗin amma sai aka gano daga bisani cewa kayayyakin sun yi ɓatan dabo a yanzu haka.

Dr. Egba Edego babban daraktan hukumar ne ya bayyana haka yayin da yake magana da manema labarai ranar Alhamis a Lafiya babban birnin jihar.

Edego yace sun kafa kwamitin ne jim kaɗan bayan ganin bidiyo da ɗan majalisar ya fitar inda ya zargi cewa an sace tabo-matattalan marasa lafiya da magoya baya da sauran kayayyakin da ya bai wa asibitin a matsayin tallafi.

Yace manufar binciken ita ce tabbatar da gaskiya da lissafi a harkar gudanar da asibitocin da kuma magance duk wani bayani na ƙarya.

A cewarsa hukumar ba ta da tsari ga sace ko karkatar da kayan asibiti. Ya jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

“Kwamitin yana da umarni na gano abin da dan majalisar ya bayar abin da ya ɓace da kuma yadda suka ɓace da kuma wanda ke da hannu a ciki,” inji shi.

Edego ya ƙara da cewa ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba domin ɗaukar matakin da ya dace.

Yace gwamnati ta zuba kuɗaɗe masu yawa wajen sanya wa asibitocin gwamnati kayan aiki domin inganta harkar kiwon lafiya.

“Taimakon da ɗan majalisar ya yi shi ne don cike gibin ƙoƙarin gwamnati. Saboda haka ba za mu jure duk wani aiki na karkatar da kayan ba,” inji shi.

Shugaban asibitin ya ƙara da cewa gwamna Abdullahi Sule ma da kansa ya umarci kwamishinan lafiya Dr. Gaza Gwamna da ya gudanar da bincike kan zargin kuma ya tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da laifi.

“Muna shirye mu ba da cikakken haɗin kai ga kwamitin da kwamishinan lafiya domin gano tushen matsalar,” inji Edego.

By ukarofi