Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ya zuwa yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa na babban taron gabatar da littafin waƙoƙi mai suna ‘Tambarin Zamani’, wanda matashiyar mawaƙiya, Salma Saeed Mailambu, ta rubuta.
Za a gudanar da taron ne a gobe Asabar 29 ga Agusta a ɗakin taro na gidan Mambayya dake Unguwar Gwammaja a cikin birnin Kano.
Ana sa ran zai samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman malamai da ɗalibai da masu nazarin waƙoƙi da al’adun gargajiyar Hausa.
Littafin Tambarin Zamani dai wasu waƙoƙi ne daga cikin fitattun waƙoƙin Salma Saeed Mailambu guda 20 aka mayar da su littafin, domin ƙara inganta harkar adabi da kuma adana shi.
Kazalika, littafin mai ɗauke da shafi 58, Dakta Murtala Uba na Jami’ar Bayero Kano ne mai sharhinsa, yayin da Dr. Aisha Mai-Mota za ta kasance mai ta’aliƙi.
Sannan littafin ya samu dubawa da gyare-gyare daga manyan masana akan harkar adabi, waɗanda suka haɗa da Dr. Ibrahim Sheme na Buɗaɗɗiyar Jami’ar Karatu ta Nijeriya (NOUN) da kuma Dakta Mujahid daga Jami’ar Jihar Kaduna.
Sarkin Mawallafan Hausa, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ne jagora na shirya gagarumin taron.
