Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
A Kano, a satin da ya gabata ne aka gudanar da zaɓen shugabannin ƙungiyar Malaman Makaranta ta ƙasa (NUT), reshen Jihar Kano, a faɗin jihar. Zaɓen ya biyo bayan ƙarewar wa’adinsu na farko a kujerunsu a ranar Litinin, 17/08/2026.
A ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, wakilan ƙungiyar malamai sun amince da sake zaɓar Kwamared Ibrahim Sale Abubakar a matsayin Shugaban ƙungiyar karo na biyu, tare da sauran masu taimaka masa, ba tare da wani abokin hamayya ba.
Zaɓen ya gudana ne a Makarantar Firamaren Nasarawar Suleimanu, cikin yanayi na tsaro, walwala da kwanciyar hankali, a ƙarƙashin sa ido na wakilan uwar ƙungiyar reshen Jihar Kano.
A bayaninsa bayan kammala zaɓen, Shugaban ƙungiyar ya nuna jin daɗinsa bisa sake amincewar da ’yan ƙungiyar suka ba shi na ya sake jagorantar ƙungiyar a karo na biyu.
Ya ce zai ƙara jajircewa wajen ganin malamai a yankin suna samun walwala da kuma duk wasu hakkokinsu da suka rataya a wuyan ƙungiyar da kuma gwamnatoci.
Kwamared Ibrahim ya ce a wa’adinsa na baya, ƙungiyar ta samar da abubuwa da dama domin ci gaban malamai a yankin, wanda hakan ya sa malamai ke zuwa aiki a kan lokaci.
Ya ce sun yi ƙoƙari wajen samar wa malamai sauƙi a harkokin da suka shafi ci gaban aikinsu, kayan karatu, tura malamai ƙarin karatu, tallafa wa marasa lafiya daga cikinsu, taimaka wa iyalan waɗanda suka rasu da dai sauran nasarori.
Ya ce, a cewarsa, waɗannan nasarori ne suka sa malamai suka ga dacewar ci gaba da ba shi damar jagorantar ƙungiyar.
Ya kuma yi kira ga gwamnati, musamman ta ƙaramar hukuma da sauran mahukunta, da su tallafa wa ƙungiyar wajen gina ofishinta, wanda ya ce aikin ya tsaya tun lokaci mai tsawo sakamakon rashin kuɗin shiga da ƙungiyar ke fama da shi.
Ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar, Hon. Nasiru Ibrahim Matage, ne ya ba su filin, tare da samun gudunmawa daga wasu al’umma domin gina ofishin na dindindin, amma sama da shekaru biyar aikin ya tsaya.
Shi ma da yake nasa bayanin, wakilin da uwar ƙungiyar ta turo domin sanya ido kan yadda zaɓen ya gudana, Kwamared Sunusi Dayyabu Minjibir, Mataimakin Shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kano, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.
Ya yi kira ga waɗanda aka zaɓa da su riƙe amanar da al’umma ta ba su wajen samar musu da abubuwan da za su inganta sana’arsu ta koyarwa.
Waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Kwamared Ibrahim Sale Abubakar, Shugaba; Auwalu Hassan, Mukaddashin Shugaba; Usman Ali Garba, Mataimakin Shugaba na 1; Haladu Danlami, Mataimakin Shugaba na 2; Abdulatif M. Sani, Mataimakin Shugaba na 3; Ali Yau, Sakatare; Muhammad Adam Umar, Mataimakin Sakatare; Abbas Haruna Abbas, Ma’ajin Kuɗi; da Muhammad Ibrahim, Sakataren Kuɗi.
Sauran sun haɗa da Bashir Garba, Sakataren Walwala; Tukur Auwalu, Sakataren Yaɗa Labarai; Ibrahim Audu, Mai Binciken Kuɗi na 1; da Rabiu Zakari, Mai Binciken Kuɗi na 2.
Sai kuma waɗanda ƙungiyar ta zaɓa domin taimaka mata na musamman a wasu harkoki: Bako Abdullahi, Mai Binciken Kuɗi na 3; Suleiman Hussaini, Mai Kula da Harkokin Rubuce-rubuce; Auwalu Shuaibu; Rabiu Auwalu Tukur; Halliru Isah; Aminu Muhammad Musa; Halima Muhammad; Sadiya Muhammad; Asabe Shehu; Na’ima Garba; da Idris Yakubu.
