Allah ya yi ma Sarkin Zurmi rasuwa

Spread the love

Dada SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Masarautar Zurmi da ke Jihar Zamfara na cikin jimami bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Bello Sulaiman Muhammad.

Majalisar Masarautar ce ta sanar da hakan a yammacin jiya Litinin.

“Allah ya karɓi ran Mai Martaba Sarkin Zurmi, Alh. Bello Sulaiman Muhammad”. Sanarwar ta ce.

Majalisar ta yi addu’o’i ga marigayin: “Ya Allah ka gafarta masa dukkan kurakuransa, ka haskaka kabarinsa ka albarkaci iyalansa”.

A cewar sanarwar, za a yi Sallar Janaza ga marigayin yau, idan Allah ya yarda.

Majiyar mu daga cikin masarautar ta bayyana cewar marigayi Alhaji Bello Sulaiman Muhammad ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya na dogon lokaci.

Kafin rasuwarsa, shi ne Sarki na 20 a tarihin Masarautar Zurmi.

A lokacin mulkinsa, an ɗauki marigayi sarkin a matsayin uba kuma mai kula da al’adu wanda ya yi aiki don inganta zaman lafiya, haɗin kai, da kuma ɗabi’un Musulunci a yankin ƙaramar hukumar Zurmi.

An san shi da haɗin kai sosai da gwamnati da hukumomin tsaro a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a masarautar.

Labarin rasuwar Sarkin ya jawo ta’aziyya daga sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci, da mazauna jihar, waɗanda suka bayyana shi a matsayin babban bango a jihar.

Har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Zamfara game da rasuwar sarkin.

By ukarofi

Leave a Reply