Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Wallahi ban da waɗanda su ka wur-wurga karin magana da sunan Ranar Hausa, sam ban ga wata riba da ranar ta cimma ba don ‘yan bazata sun yi kaka-gida musamman a taron da a ka gudanar a gidan Mambayya da ke Kano. Da an kawo maganar ƙabilanci sai ka ji zallawa sun ɓarke da tafi raf-raf-raf kamar tafin hannunsu na katako ne
Da alamu akwai waɗanda ko don siyasa ko kawai ganin shafuka barkatai a yanar gizo na Zallawa, ya sa su ka ɗauka ko mutanen nan masu iƙirarin su Huasawa ne zalla, na da wani amfani ko tasiri har za ka ga wanda ba kayi tsammani ba wai ya na taya al’ummar Hausawa ranar Hausa! Yaushe al’ummar Hausawa su ka zauna su ka ayyana rana don Hausa? Kai ruɗewa da muradun siyasa kan sa ɗaukar matakai masu ban al’ajabi.
Na ga wanda ko wadanda su ka yi faifan bidiyo wai su na taya Hausawa murnar ranar Hausa. Yaushe miliyoyin Hausawa su ka ware irin wannan rana? Kai wani har tabarau zai maƙala a idonsa amma in ya tabka wata kwaba sai ka ga tamkar ko ajin A B C D bai taba shiga ba. Jawabin da Sheikh Ibrahim Khalil ya yi a taron Mambayya sam bai burge Zallawa ba don ya ce “Hausawa sun zama al’umma sun fi ƙarfin ƙabila” ya na mai cikawa da cewa kuma da wuya a samu Bahaushe tsantsa.
Batun za a nuna al’adun Hausawa daga taron masu sanya hula hana-sallah, waƙa ko rawa da dambe duk ai ba wani tasiri da hakan ya yi duk da kawai wasu ne ke magana har da jawo aya ko hadisi a tsakanin mutanen da ke tutiyar ƙABILA TA FI ADDINI da masu cewa AN DAINA YAUDARARSU DA ADDINI kazalika da masu cewa su na da Kirista a cikinsu amma ko aya ɗaya tak a Baibul ba wanda ya ja don tsananin makircin mannewa a jikin Musulunci don yaudarar al’ummar Hausawa na gaskiya.
Kai taron mai wasa da kura ko maciji a gefen kasuwa ya fi wannan taro na waɗanda ke ɓoye kansu a soshiyal midiya su na zagin malaman Musulunci . Haƙiƙa ba wani abu na sisin kobo da Hausawa su ka amfana da shi a taron sai rawar koroso, farafaganda da ɓarkewa da tafi raf-raf-raf-raf daga waɗanda da alamu ba su saba zuwa taruka ba don haka su ka birkice.
Shin wane dattijo ne ko wane masani ne na gaske ya halarci taron Zallawa kuma menene abu ɗaya tak da ya shafi bunƙasa harshen Hausa da taron ya cimma? Tabbas Zallawa da alamu sun sauya wasu abubuwan da su ka tsara yin a dabdala don haska makircinsu da tocila mai batur 18.
Tun bara na ke ganin wasu na amfani da ƙirƙirarriyar rana da wasu ‘yan soshiyal midiya su ka yi da sunan ranar Hausa wajen rubuta karin magana da wasa kwakwalwa, azancin zance da sauran su. Hakika ba laifi ba ne bunƙasa karin magana don hakan zai taimakawa matasa masu tasowa su san wasu kalamai na kwarewa na harshe.
Ni a wajena in za a samu wata rana don tattaunawa kan ADABI ko kwarewar harshe ba laifi ba ne amma kash Zallawa sun fauce lamarin don harkar haddasa fitinar ƙabilanci da kwangilar AIFOB da cire Arewa ta tsakiya daga kokuwar Arewa wai Midil Bel ne.
Ina kira ga duk Hausawa su yi takatsantsan da makiya Hausa da Musulunci da ke shigar burtu don kammala murkushe Lardin Arewa.
Yo wanda ya ke saka hana-sallah amma wai shi ne zai nuna tufafin gargajiya na Hausawa ko mai ɓoye suna da adireshi amma ya na fakewa da sunan ranar wajen zagin Shehu Mujaddadi da aibata malaman Musulunci.
Shin yaya ma wani Bagware zai ce wai zai nuna gasar waƙa ko rawa ko dambe da fakewa da lokacin da ya dace a yi jawabai na ilimi da ƙarfafa dogaro da kai.
Zallawa ba za su cimma burinsu na wargaza Arewa ba har abada.
Duk mai gayyatar wai ranar hausa wa in ma yaro ne ɗan lakada-kawas, bagware ko dan kwangila
Kawai wasu ‘yan zamanin taliyar indomie rangai-rangai ba sa ko iya magana da ingantacciyar Hausa ba wurga Turanci, su hau yanar gizo wai sun ƙirƙiro ranar Hausa ta duniya, iyye ka ji karambani, wa ya aike su? Yo Hausa tun kafin kakanninsu ina ne ba ta shiga ba a duniya?.
Wace rana ce kai har dare ma da ba a yi na Hausa a baya ba? To wai za su bunkasa Hausa ko harshen Hausa! Shin Hausa ce za ta bunƙasa su ko su ne za su bunƙasa Hausa? ’Yan barandar AIFOB ne ma su ka fi zama marar sa hangen nesa don ba yadda za su iya aiki da harshen Musulunci su wargaza Arewa don kafa Biyafara da tsame wani yanki wai Midil Bel daga Arewa.
Ban da fatake da su ka shiga duniya ta gabar da yamma a tsohon tarihi, mu ɗau kafafen labaru kaɗai na duniya tun 1957 ƙasar ’yan mulkin mallaka Burtaniya ta dau Hausa a matsayin harshe na farko na Afurka da ta fara shirye-shirye da shi. Amurka ta ɓullo da sashen Hausa a 1979. Jamus ta ɓullo da sashen Hausa a 1963. Tsohuwar tarayyar Sobiyet ra buɗe sashen Hausa 1961. Faransa ta buɗe sashen Hausa Rfi a 2007. ƙasar Sin ta buɗe sashen Hausa 1961. Turkiyya ta buɗe TRT Hausa a 2023.
Wannan fa ban da rediyon Garwa/Garoua a Kamaru, Rediyon Kirista na ELWA a Laberiya 1954. Rediyon Jamhuriyar M√sulunci na Iran da rediyon Muryar Afurka a birnin Alkahira na Masar da mu ka yi ta aika saaonni wajen su Mustapha Ibrahim, Musa Muhammad Isa da Sa’ad Zannur Abubakar. Kazalika ai na kawo mu ku shiga da na yi sashen Hausa na kafar labarun haramin Makkah.
Wallahi harshen Hausa ba zai karu da komai ba daga taron Zallawan nan fa sai shirme, makirci da kaskanci, lalaci da sakarci. Harshen nan ya fi gaban wani wai ya ware rana wai za a yi nunin kayan gargajiya, za a yi waka ko rawa ko gasar dambe.
Shin mai sa hula hana-sallah shi ne zai nuna kayan gargajiya in ba rainin wayo ba? Waka ko rawa ai kullum ma a na yi a fina-finan Kannywood da filayen gurmi, garaya da fagen ‘yan Gambara, oh Allah ya jiƙan Alhaji Musa Na Saleh mai kaset. Shin nunin dambe ai kullum a na yi a gidajen dambe ba wata sana’a ce da ke neman mutuwa ba balle wani dɗan koroso ya ce zai farfaɗo da ita.
Wallahi waɗannan Zallawan sun raina Hausa da Hausawa don ba su ma fahimci me Hausa ba balle har su iya shigar burtu da harshen don cimma burin kwangilarsu ta haddasa fitina tsakanin Musulmi. KANAWA GA KU NAN GA ZALLAWA illa iyaka.
Uwar ɗakin Zallawa Hauwa Mundi ta kara tabbatar da Gidauniya ce zallawa su ka yi wa rejista ba ƙungiya ba. Duk gaggan Zallawa ma da Gidauniya su ke fahari don sun san ƙungiyar Hausawa ta fi karfin iyayensu da kakannninsu
Shin tsakani da Allah yau na fara batun ba wata ƙungiya sam-sam wai ta HAUSAWAN NIGERIA? Kakaf ba a taba yi wa wannan ƙungiya rejista ba amma wasu ‘yan kwangila sun yunkura a 2022 su ka shiga hukumar rejistar kamfanoni CAC su ka samu yin rejistar GIDAUNIYAR HAUSAWA DEɓELOPMENT ASSOCIATION da fakewa da za su riƙa aikin tallafawa ‘yan gudun hijira da jinkai, amma sai su ka tsunduma kamfen ɗin zagin Shehu Mujaddadi, wulakanta mai alfarma Sarkin Musulmi, cin zarafin manyan malaman Musulunci da ruruta wutar fitinar ƙabilanci a tsakanin Musulmi.
Uwar dakin Zallawa Hauwa Mundi daga jihar Neja ta yi wa kanta baji na yanar gizo da wannan GIDAUNIYA da abun takaicin ma rabin sunan ma duk Turanci ne da hakan ke nuna ‘yan arufta ne da ko a makaranta sun ɗauka kauyanci ne karanta Hausa sai yamutsa gashin baki da gatsine da sunan furta kalmomin Turanci don burge ‘yan kudu da Yammawa. Kan ka ce me ye, sai yara mabiya Mundi su ka riƙa zagaye hotunansu da wannan bajin ta manhajar da su ka tsara. Gaskiya ba ta neman ado kuma duk tsawon dare gari zai waye.
Wayon Zallawa a nan bayan babban rubutu na GIDAUNIYA sai su lankaya ɗan ƙaramin rubutu a gefe mai sunan HAUSAWAN NIGERIA nan ma da ɗaukar DAGIN AREWA da Sardauna ya tsara a sabon zamani. Kai hatta gayyatar taron nan na ranar Zallawa, da sunan Gidauniya su ka yi shi don ba mahalukin da zai samu dama tsigau-fiyau a yi ma sa rejistar ƙungiya a madadin miliyoyin Hausawa.
KAMMALAWA
‘Yan Gidauniya har shafin talabijin na yanar gizo su ka kafa da sunan GIDAUNIYA Tɓ sai wani ɓoyayyen Bazalle mafi jin tsoro mai sunan bagaye na Larabawa ya kafa Hausa Zalla Tɓ kamar yadda ya taba yi a shafin GIMBIYAR HAUSA da kan yayata faya-fayan ta’addanci da sharri da kuma buɗe kafa don ‘yan AIFOB su ruruta fitina a Arewa don wargaza yankin don samun kafa Biyafara a bulus lumus sai kuma nesanta ƙirƙirarren yanki Midil bel daga Arewar Musulmi. Shin karatun ya fito fes-fes ko da saura?
