Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta bai wa kamfanoni 31 da suka yi nasarar lashe rijiyoyin mai da iskar gas 37 a zagayen bayar da lasisin haƙar mai na shekarar 2025 wa’adin kusan kwanaki 60 domin biyan kuɗaɗen da ake buƙata, ko su yi asarar lasisin da aka ba su na wucin gadi.
Gargaɗin ya zo ne wata guda bayan gudanar da taron tantancewa da bayar da lasisin kasuwanci da aka yi a Abuja ranar 21 ga Yuli, 2026, inda aka sanar da sunayen kamfanonin da suka yi nasara a gasar neman rijiyoyin.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, NUPRC ta ce kamfanonin da suka yi nasara sun fara cika sharuɗɗan da aka gindaya, bayan an ba su takardun lasisin wucin gadi. Hukumar ta gargaɗi waɗanda suka yi nasara cewa duk wanda ya kasa biyan kuɗaɗen cikin wa’adin da Dokar Masana’antar Man Fetur ta Nijeriya (Petroleum Industry Act) ta tanada, zai rasa kuɗin jinginar da ya bayar domin tabbatar da tayinsa, sannan a mika rijiyar da aka ba shi ga kamfanin da ya zo na gaba a jerin masu jiran gado.
A ƙarƙashin ka’idojin zagayen lasisin, kamfanonin da suka yi nasara ana buƙatar su biya kuɗin lasisin farko, wato signature bonus, wanda ya kasance tsakanin dala miliyan uku zuwa dala miliyan bakwai kan kowace rijiyar mai da gas. Baya ga haka, akwai kuɗaɗen hayar rijiyar na shekarar farko, jingina da sauran sharuɗɗan da kamfanonin za su cika bayan samun lasisin.
A bisa doka, kamfanonin suna da kwanaki 90 daga ranar da aka ba su lasisin wucin gadi domin kammala biyan kuɗaɗen. Saboda haka, sabon gargadin NUPRC na nuna cewa kusan kwanaki 60 ne suka rage wa kamfanonin domin su kammala biyan kuɗaɗen da ake buƙata. Idan aka yi la’akari da ranar 21 ga Yuli, 2026 da aka bayar da lasisin, wa’adin ƙarshe na biyan kuɗaɗen zai kasance 19 ga Oktoba, 2026.
NUPRC ta ce duk kamfanin da bai cika sharuɗɗan cikin lokacin da doka ta ƙayyade ba zai rasa lasisin da aka ba shi kai tsaye, sannan a mika shi ga kamfanin da aka ayyana a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Rijiyoyin mai da iskar gas 37 da aka bayar sun bazu a yankunan Neja Delta, yankunan ruwa mara zurfi da zurfin teku, da kuma wasu sabbin yankunan da ake sa ran gano albarkatun mai. Rijiyoyin sun haɗa da waɗanda ke cikin Basin na Benin, Basin na Anambra, Basin na Chadi da Benue Trough, baya ga wata rijiyar da ke cikin zurfin teku.
Kamfanoni 143 ne suka shiga gasar neman lasisin, inda suka gabatar da kusan tayin neman rijiyoyi 200 daga cikin rijiyoyi 37 da aka yi takara a kansu. Sai dai daga cikin rijiyoyi 50 da aka fara gabatarwa domin neman masu zuba jari, guda 13 ba su samu ko tayin kamfani ɗaya ba.
