
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tawagar shari’a ta jam’iyyar APC a Jihar Osun da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Adebayo Adedamola a zaɓen gwamna na 15 ga Agusta, sun yi watsi da iƙirarin cewa sun shigar da wani ƙorafi da ke ƙalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke a kotu.
Wannan na zuwa ne bayan da aka wallafa wasu takardu a ranar Litinin a allon sanarwar kotun ƙorafin zaɓen gwamnan jihar da ke cewa na ƙorafe-ƙorafen APC da PDP ne. Rahotanni sun bayyana cewa wannan ci-gaba ya haifar da ruɗani game da ainihin inda aka samo ƙorafe-ƙorafen, inda kotun ta ce an shigar da su ne daga jam’iyyun biyu kan sakamakon zaɓen gwamnan.
Sakataren kotun, Pefe Belemore ne ya tabbatar da ƙorafe-ƙorafen da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen na ranar 15 ga Agusta. A ƙorafin mai lamba EPT/OS/GOV/01/2026, an zayyano Bola Oyebamiji da APC a matsayin masu ƙara, yayin da Adeleke, Accord Party, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kuma sune masu kare ƙara. A na biyun kuma mai lamba kamar haka: EPT/OS/GOV/02/2026, Adedamola ne ya shigar da su INEC, Accord da kuma Adeleke ƙara.
Saidai, kwamitin shari’ar APC ya ce sam bai shigar da wani ƙorafi ba na ƙalubalantar nasarar Adeleke, yayin da Adedamola shi ma ya ce babu wanda ya shigar da ƙara kan gwamnan daga ɓangarensa ko kuma lauyoyinsa.
Daya daga cikin jagororin kwamitin shari’ar na ɗan takarar APC, Adekunle Adegoke (SAN) ya shaida wa PUNCH a ranar Litinin cewa lauyoyi sun shawarci Oyebamiji akan kada ya tunkari kotun ƙorafin bayan zaɓen. Ya ce, sun gana da ɗan takarar APCn da jagororin jam’iyyar kuma sun amince ba za su ɗauki matakin shari’a ba saboda maslahar jihar da zaman lafiyarta.
Haka ma ɗan takarar PDP, Adedamola ya musanta shigar da ƙorafi kan al’amarin ko bayar da damar a shigar a madadinsa, a lokacin da yake hira da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin.
Adeleke dai ya lashe zaɓen Osun ne na 15 ga Agusta, 2026 bayan samun ƙuri’a, 511,067, lamarin da ya mayar da shi kan kujerar mulkin jihar a karo na biyu tun bayan zaɓar sa a 2022.
