
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama wani ɗan shekara 35 mai suna Adamu Musa wanda ke iƙirarin shi ɗan sanda ne mai muƙamin CSP, wato Babban Sufuritandan ‘Yan sanda bisa hannu a damfara da aikin sojan gona.
Wanda ake zargin, wanda ɗan yankin Kureken Sani Quarters ne a Kano da ke zagayawa yana damfarar al’umma, an bayyana shi ne ga manema labarai ta ofishin Kakakin rundunar, CSP Haruna Abdullahi Kiyawa, a ranar Talata.
Haruna Kiyawa ya bayyana cewa, a ranar 1 ga Satumba, 2026 ne rundunar ta samu wani kira na gaggawa daga sashen ‘yan sandan na musamman – No. 52 Police Mobile Force da ke Challawa a Kano. Akan haka ne aka tura jami’ai daga yankin babban ofishin rundunar na Panshekara sakamakon samun wasu bayanan sirri, inda suka kama wanda ke iƙirarin shi ɗin CSP ne na hukumar.
Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin, ya ƙware wajen damfarar al’umma da sunan cewa shi babban jami’i ne kuma yana da ƙafa a harkar ɗaukar aikin ɗan sanda da tura jami’ai gurin aiki.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya kuma ce, mutumin da ake zargin ya yi wa wasu hotuna kwaskwarima da gabatar da kansa ta fasahar AI a matsayin shi ɗin babban jami’i ne na rundunar ‘yan sanda. Ya fe, yana amfani da waɗannan hotuna ne wajen nuna cewa yana da alaƙa da wasu manyan jami’ai domin samun sauƙin damfarar mutane wajen tura masa kuɗin samar da aiki da na sauya wajen aiki.
Daga cikin ababen da hukumar ta ƙwato akwai baƙar rigar ‘yan sanda, baƙin takalmin aiki, kakin ‘yan sanda baƙi da shuɗi da tsabar kuɗi N300,000 yayin atisayen. A cewar Kiyawa, ana tsare da shi a komar hukumar kuma da zarar an kammala bincike a kansa, za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Kazalika, jami’in hulɗa da jama’ar ya gargaɗi al’umma da su riƙa kasancewa a ankare da ‘yan damfara da masu aikin sojan gona, wanda suke amfani da fasahar AI wajen samar da hotunan bogi na manyan jami’an da nufin tatsar kuɗi daga hannun mutane da sunan samar da aiki ko sauya wajen aiki.
A ƙarshe, ya ce babu wani kuɗi da ake karɓa da sunan nema wa mutum aiki ko canza wa jami’i wajen aiki, yana mai shawartar mazauna da su riƙa kai ƙarar dukkan wanda aka samu yana iƙirarin shi ɗan sanda ne ga ofishin hukumar mafi kusa.
