Mai shekaru 87 ya sari alƙali da adda a cikin kotu bisa zargin ba zai samu adalci ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani tsoho mai shekaru 87 ya sari alƙalin wata kotu da adda a yayin da ake tsaka da shari’a a yankin Mayo-Ine da ke ƙaramar Hukumar Fufore a Jihar Adamawa.

Rahotanni sun ce Dahiru Garba ya far wa alƙalin, Dauda Hamman, da adda ne a lokacin da yake jagorantar shari’ar da ake yi tsakanin dattijon da wani mutum mai suna Ismail Yusuf, bisa zargin cewa ba zai samu adalci ba.

An ce tsohon ya rika sarar alƙalin da addar sau da dama, lamarin da ya jawo masa munanan raunuka, ciki har da yanke masa hannu. A halin yanzu, alƙalin yana karɓar magani a wani asibiti da aka kai shi domin samun kulawa.

ɗahiru Garba, wanda ya fito daga ƙauyen Korawa da ke gundumar Mayo-Ine, an kama shi tare da gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Majistare ta 1 da ke Yola a ranar Litinin.

A lokacin da yake amsa tambayoyin kotu, Dahiru ya ce, “Shaidan ne ya sa ni,” ya aikata wannan abu, tare da nuna nadama kan abin da ya faru.

ASP Zakka Musa, wanda ya gurfanar da shi, ya gabatar wa kotun da Rahoton Farko na ’Yan Sanda, inda wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya aikata laifin.

Mai gabatar da ƙarar ya shaida wa kotun cewa an tura batun daga Hedikwatar ’Yan Sandan Fufore zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) a ranar 4 ga Satumba, 2026, domin ci gaba da bincike.

Manhaja ta ruwaito daga Gaskiya News Hausa cewa, a cewar ’yan sandan, Alƙali Dauda Hamman ya kai rahoton lamarin Ofishin ’Yan Sanda na Mayo-Ine a ranar 31 ga Agusta, 2026.

Ya bayyana cewa yana jagorantar wata shari’a ne lokacin da Dahiru Garba, wanda ke cikin waɗanda ake ƙara a shari’ar, ya taso masa da adda ba zato ba tsammani.

Bayan an karanta wa Dahiru bayanan da ke cikin Rahoton Farko na ’Yan Sanda, ya amsa cewa shi ne ya aikata abin da ake zarginsa da shi.

Daga nan ne kotun, ƙarƙashin jagorancin Babban Alƙalin Majistare, Ismail Bello Shelleng, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali da ke Yola.

Ana zargin Dahiru da aikata laifin haddasa mummunan rauni, wanda ya saɓa wa Sashe na 219 na Dokar Penal Code ta Jihar Adamawa ta shekarar 2018.

Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga Satumba, 2026, domin ci gaba da sauraron lamarin.

Lamarin ya jawo hankalin jama’a, musamman saboda shekarun wanda ake zargin da kuma yadda harin ya faru a cikin kotu yayin da ake gudanar da shari’a.

By ukarofi