‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga 18 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Haɗin gwiwa na jami’an tsaron CWC, ‘yan banga da ‘yan farauta sun kashe ‘yan bindiga 18, sun ƙwato bindiga biyu ƙirar AK 47 a ƙauyen Gidan Iyabo a garin Kakuma na ƙaramar hukumar Bakori.

Kwamishinan cikin gida da tsaro a Jihar Katsina, Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa wanda ya fitar da sanarwar haka ya bayyana cewa waɗannan jami’an tsaro sun sami wannan nasara ne bayan samun bayanan sirri na yunƙurin kai mummunar hari ƙarƙashin gawurtaccen ɗan ta’adda Musa Dala wanda tsohon shugaban makarantar Firamare (Headmaster).

Shi wannan tsohon Headmaster a cewar Dr Ɗanmusa yana da sansanin sa a dajin Mununu da ke ƙaramar hukumar Faskari.

Jami’in tsaron sun ƙwato bindiga guda uku ciki har da ƙirar AK 47 guda biyu da harsashi da kuma babura guda uku.

Akwai kuma shanu biyu da dabbobi 94 da ‘yan bindiga suka yi ƙoƙarin sace wa.

Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Raɗɗa ya jinjina wa jami’an tsaro da suka daƙile yunƙurin kai wannan hari da kuma ƙwarewar da jami’an suka nuna wajan tunkarar ‘yan bindigan.

Gwamnan ya bayyana cewa haɗin gwiwa na jami’an na sojoji, DSS, ‘yan sanda sun shiga farauta sauran wannan mahara a duk inda suke a yankin da jihar baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply