Gombe 2027: A kawo muƙabala, Gwamna na nan a shirye – Shawai

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dakta Jamil Isyaku Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya ce ɗan takaransa a shirye yake ya fuskanci sauran ’yan takarar gwamna a muƙabalar bainar jama’a gabanin zaɓen 2027.

Shawai ya ce duk wanda ke kiran a gudanar da muƙabalar ya sanya rana da wurin da za a yi ta, domin a cewarsa, Gwamna “a shirye yake kowace rana, a kowane lokaci.”

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce muƙabalar za ta ba ’yan takarar damar gabatar da manufofinsu da tsare-tsarensu tare da bayyana yadda za su tunkari ƙalubalen da ke gaban jihar.

Sai dai ya jaddada cewa bai kamata muƙabalar ta zama wajen musayar zarge-zarge, ƙarya ko farfaganda ba, illa dai ta mayar da hankali kan abin da ’yan takara suka aikata, ƙwarewarsu da abin da suke shirin yi wa jama’a.

“Jagoranci ya fi muƙabala, yawan magana, zarge-zarge marasa tushe, ƙarya da farfaganda girma. Siyasa da mulki ba gasar kalamai ba ce. Jagoranci ya shafi mutane, alaƙa, ƙwarewa, gogewa, hukumomi da sakamako,” in ji Shawai.

Ya ce Gwamna ya shafe sama da shekaru 20 yana gina alaƙa a faɗin Gombe da wajen jihar, tare da tallafa wa mutane da kuma samar da hanyoyin hulɗa a tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.

A cewarsa, irin wannan tarihi ya kamata a fito da shi fili domin jama’a su tantance tarihin ayyukan dukkan ’yan takarar da ke neman shugabancin jihar.

Shawai ya ce muƙabalar ya kamata ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar jama’a, ciki har da ayyukan yi, ilimi, kiwon lafiya, noma, ruwan sha, ababen more rayuwa, zuba jari, masana’antu, matasa da ƙarfafa mata.

Ya kuma yi ikirarin cewa Gwamna ya taka rawa wajen samar da guraben aikin yi sama da 1,800 ga ’yan asalin Gombe a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano, KEDCO.

Ya ƙara da cewa an samar da sama da guraben aikin yi 1,000 a hukumar samar da ruwan sha ta Jihar Gombe, tare da wasu shirye-shiryen tallafin karatu, tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da ƙarfafa matasa da mata.

Dangane da shirin mulkinsa, Shawai ya ce ajandar Gwamna ta dogara ne kan ci gaba da ayyukan gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, da tabbatar da ɗorewar su da faɗaɗa su.

Ya ce tsarin ci gaban Jihar Gombe na shekaru 10 ya kamata ya kasance ginshiƙin ci gaba, ba tare da la’akari da sauyin shugabanci ba.

“Gwamnati ci gaba ce. Ci gaba na buƙatar manufofi masu ɗorewa, ba wai a riƙa watsar da abin da aka fara ana komawa daga tushe a duk lokacin da shugabanci ya sauya ba,” in ji shi.

Shawai ya kuma ƙalubalanci sauran ’yan takara da su fito da sahihan bayanan ayyukan da suka yi a baya, maimakon dogaro da alkawuran yaƙin neman zaɓe kawai.

“Mu sanya tarihin ayyukanmu a gaban jama’a. Mu yi muƙabala kan ayyuka, ba kalamai ba; kan tasirin ayyuka, ba farfaganda ba; kan mutane, ba alkawura kawai ba,” in ji shi.

Ya sake jaddada cewa ɗan takarar APC a shirye yake ya tattauna kan tarihinsa, hangen nesansa da tsare-tsarensa a duk wani dandali da za a haɗa shi da sauran ’yan takarar gwamna.

By ukarofi

Leave a Reply