Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Daraktan-Janar na hukumar gyaran ayyukan gwamnati (BPSR), Mista Dasuki Ibrahim Arabi, ya yi kira da a ƙarfafa cibiyoyin gwamnati tare da samar da sahihan bayanan bala’o’i a kan lokaci, domin bai wa Najeriya damar mayar da martani yadda ya kamata ga aukuwar ibtila’i da sauran abubuwan gaggawa.
Arabi ya yi wannan kiran ne a taron shekara-shekara na Emergency Response and Simulation Summit 2026, wanda aka gudanar a Abuja, inda aka karrama shi da lambar girmamawa ta Fellowship saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen gyaran ayyukan gwamnati da bunƙasa cibiyoyin gwamnati.
A yayin taron, an kuma ƙaddamar da ECRMI Real-Time Disaster Data Management System Platform, wani tsarin zamani da aka samar domin inganta samun bayanan bala’o’i cikin lokaci tare da ƙarfafa amfani da fasaha wajen gudanar da ayyukan agajin gaggawa.
Arabi ya ce ƙaruwar yawaita da sarƙaƙiyar aukuwar ibtila’i na buƙatar hukumomi su daina dogaro da martani bayan faruwar lamarin kawai, su maida hankali wajen samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen hango haɗura tun kafin su faru da kuma ɗaukar matakin gaggawa.
Ya ce sahihan bayanan bala’o’i na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tsarin gargaɗi na farko, inganta rabon albarkatu da kuma tabbatar da ingantaccen haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke da alhakin agajin gaggawa.
Ya ce: “Gudanar da al’amuran gaggawa bai kamata ya taƙaita ga mayar da martani bayan faruwar wani lamari ba. Ya kamata a samar da cibiyoyi masu shiri, masu saurin ɗaukar mataki, masu haɗin kai da kuma juriya.”
Shugaban BPSR ya bayyana dandalin ECRMI a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen amfani da fasaha don inganta shirin tunkarar bala’o’i, amma ya jaddada cewa fasaha kaɗai ba za ta iya tabbatar da ingantaccen martani ba.
A cewarsa, dole ne a haɗa fasaha da gyaran hukumomi, fayyace nauyin da ya rataya kan kowace hukuma, horar da ma’aikata, samar da tsarin da zai bai wa hukumomi damar musayar bayanai cikin sauƙi, da kuma tabbatar da gaskiya da ingantaccen tsarin tafiyar da bayanai.
Arabi ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki su inganta tsarin musayar bayanai cikin gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da tsaro, ingancin bayanan da kuma yadda ya kamata a yi amfani da bayanan bala’o’i.
Ya yi kira da a rungumi tsarin haɗin gwiwar gwamnati baki ɗaya da kuma al’umma baki ɗaya, wanda zai haɗa hukumomin gwamnati, al’ummomi, jami’o’i da masana, kamfanonin fasaha, ƙungiyoyin ci gaba da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
A cewarsa, sauye-sauyen zamani ta fuskar fasahar sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire, inganta ayyuka da kuma ƙara ƙarfin hukumomi na daga cikin muhimman ginshiƙan gyaran ayyukan gwamnati.
Ya ce babban ma’aunin nasarar duk wani shiri na sauya tsarin tafiyar da gwamnati ta hanyar fasaha shi ne yadda yake taimakawa wajen inganta yanke shawara, ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma samar da ingantattun ayyuka ga ’yan ƙasa.
Arabi ya sake tabbatar da ƙudurin BPSR na ci gaba da inganta ingancin hukumomi, ƙirƙire-ƙirƙire, riƙon amana da kuma inganta ayyukan gwamnati ga al’umma.
