Daga JAMIL GULMA a Kebbi
An yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani (Social Media) da ke ƙarƙashin jam’iyyar ADC da su tabbatar da sahihancin labarai kafin yaɗawa da kare mutuncin juna.
An gudanar da wannan taron wayar da kai ne a ƙarƙashin jagoranci Argungu New Media Actors.
Taron wanda ya haɗa masu amfani da kafafen sada zumunta na kafafen sada zumunta da ke aiki ƙarƙashin jam’iyyar ADC domin ƙara fahimtar juna da wayar da kai kan muhimmancin amfani da kafafen sadarwa.
A wajen taron mai taken “Gaskiya da mutunta ra’ayin siyasa”, Shugaban yaƙin neman zaɓe na ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Alhaji Mansur Adamu Gulma ya bayyana yadda za a yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yaɗa sahihan bayanai, ilimantar da jama’a da kuma inganta sadarwa, tare da kaucewa yaɗa labaran ƙarya, ɓata suna, cin mutunci da yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancin su ba.
Ya bayyana cewa ba sai an yi wa kowa ƙazafi ba illa dai a cigaba da yaɗa manufofin jam’iyya da kuma ‘yan takara.
Taron ya yi ta ƙarin haske kan bincike da tabbatar da sahihancin labari kafin a wallafawa ko yaɗawa, domin gujewa ƙirƙira ko yaɗa labaran ƙarya kanzon kurege tare da mutunta mutane da ra’ayoyin su domin gujewa kalaman batanci hadi da cin zarafi da ɓata sunan juna a kafafen sadarwa na zamani.
A cikin jawaban masana Kafar sadarwa sun kara da cewa ayi Amfani da kafafen sada zumunta tamkar wajen ilimantarwa da wayar da kai tare da gina kyakkyawar muhawara ta siyasa ba tare da ƙiyayya ko cin mutunci ba.
An jaddada cewa bambancin ra’ayin siyasa ba ya kamata ya zama dalilin ƙiyayya ko cin mutunci ba,domin kafafen sada zumunta za su iya zama muhimmiyar hanya ta tattaunawa, ilimantarwa da haɗa kan al’umma idan a ka yi amfani da su yadda ya kamata.
Taron ya samu halartar wadansu daga cikin shugabanni da masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da Honarbul Mansur Adamu Gulma Shugaban yaƙin neman zaɓe na ƙaramar hukumar Argungu, mataimakin shugaban matasa na jam’iyar ADC, Ciyaman, APC New Media Actors Kebbi State,Muktar Alhassan Ɗan Mukhtar Dan Baturiya ,Ma’ajin new media matakin jiha,da kuma Uthman M Jibo ,Sakataren jin daɗi na mataki na Jiha, Mubarak Bala Umar OC ɗan karamin su babban su da Aminu Saidu da kuma Shugabar mata Hajiya Umma Shu’aibu da Hussaina Umar da kuma A’isha Utono.
