Ma’aikata sun ayyana shiga yajin aikin gargaɗi daga 2 Oktoba kan matsin tattali

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatan gwamnati ƙarƙashin Haɗakar Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnatin ta Ƙasa (JNPSNC), ta ayyana tsunduma a yajin aikin gargaɗi na kwana uku daga ranar 2 zuwa 4 Oktoba, 2026 kan abin da suka kira da “ƙamarin matsin tattali da lafiyar ƙwaƙwalwa” da ke addabar ma’aikata da abin da suka dogara da shi.

Majalisar ta umarci jagororinta na ƙasa da jihohi da su haɗa kan ma’aikata domin shiga yajin aikin, wanda za a fara da tsakar daren Juma’a 2 ga Oktoba kuma ya ƙare a ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026.

Rahotanni sun ce, wannan mataki ya biyo bayan buƙatar da ma’aikata suka gabatar wa gwamnati na ta ɗauki matakin rage musu raɗaɗin wahalhalun rayuwa a sanadiyyar matsin tattali, ciki har da rage farashin fetur, biyan su bashin albashinsu da fara tattaunawa akan sabon mafi ƙarancin albshin ma’aikata.

Wannan umarni na ƙunshe ne a wata takarda mai 1 ga Oktoba a matsayin kwanan wata da Sakataren JNPSNC, Ollwoyo Gbenga ya sanya wa hannu, wanda ya yi kira ga jagorancin da ya tabbatar cewa saƙon ya isa ga dukkan ma’aikata a faɗin Nijeriya.

A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan zargin Gwamnatin Tarayya da gaza warware matsalolin da aka gabatar wa Shugaba Bola Tinubu a wata wasiƙa mai kwanan wata 21 ga Satumba, 2026. Akan haka ne JNPSNC ta yi kira ga ma’aikatan gwamnati a matakin tarayya, jiha da ƙananan hukumomi da su shiga yajin aikin, tana mai cewa za ta yi hakan ne domin ankarar da gwamnati kan wahalhalun da ma’aikata suke fuskanta a sassan ƙasar.

Ta kuma bayyana halin a matsayin abin da ke ƙara ƙamari ga ma’aikata da ke jefa su cikin mawuyacin hali a zamantakewar yau da kullum, tana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mayar da farashin litar fetur zuwa N500 da kuma amincewa da biyan bashin albshin da suke bi. Kazalika, ta buƙaci gwamnatin da kafa kwamitin samar da sabon mafi ƙarancin albshin da bai gaza N500,000 ba daga 2027.

By Babaji

Leave a Reply