Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan Appropriation (Amendment) (No. 4) Bill, 2025, wanda ya ƙara wa’adin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 daga ranar 30 ga Satumba, 2026 zuwa ranar 31 ga Disamba, 2026.
Matakin ya biyo bayan amincewa da gyaran da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka yi a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, kafin a tura ƙudirin ga Shugaban ƙasa domin sanya hannu.
A cewar wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Laraba, tsawaita wa’adin zai bai wa Ma’aikatu, Hukumomi da Sassa na Gwamnati (MDAs) ƙarin lokaci domin kammala ayyukan manyan gine-gine da sauran ayyukan raya ƙasa da ake ci gaba da gudanarwa.
Sanarwar ta ce matakin zai kuma tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen da aka ware a kasafin kuɗin yadda ya kamata, ba tare da kawo cikas ga muhimman shirye-shiryen gwamnati ba.
“Tsawaita wa’adin zai bai wa Ma’aikatu, Hukumomi da Sassa na Gwamnati ƙarin lokaci domin kammala ayyukan manyan gine-gine da ake ci gaba da gudanarwa,” inji sanarwar.
Ta ƙara da cewa matakin zai taimaka wajen tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka riga aka ware sun yi amfani ga al’umma, tare da kauce wa kawo cikas ga muhimman shirye-shiryen gwamnati.
Shugaba Tinubu ya yaba wa shugabanni da mambobin Majalisar Dokoki ta ƙasa bisa yadda suka gaggauta duba tare da amincewa da gyaran kasafin kuɗin, yana mai cewa hakan na nuna ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa domin amfanin ƙasa.
Da wannan gyara, Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗin 2025 har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2026, maimakon wa’adin da ya ƙare a ranar 30 ga Satumba.
Wannan shi ne karo na huɗu da aka tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren manyan ayyuka na kasafin kuɗin 2025, bayan an taɓa ƙara wa’adin zuwa Maris, sannan Yuni, daga bisani zuwa Satumba kafin sabon tsawaitawar da ta kai wa’adin zuwa Disamba.
