Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, yana mai cewa siyasa na iya yin tasiri wajen bincike da gurfanar da wasu mutane.
Sarkin ya kuma yi magana kan shari’a da kuma ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai tambayar ko yadda ake gudanar da wasu shari’o’in cin hanci da rashawa ya dace da manufar da aka kafa hukumomin yaƙi da rashawa domin cimmawa.
Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a Lagos.
Ya ce samar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa kaɗai bai isa ba, matukar hukumomin da ke da alhakin bincike, gurfanarwa da yanke hukunci ba sa aiwatar da su yadda ya kamata.
Ya ce an samu lokutan da aka yi watsi da wasu tuhume-tuhumen cin hanci saboda waɗanda ake zargi suna da alaƙar siyasa ko kuma goyon bayan manyan ’yan siyasa.
Sarkin ya ce irin wannan yanayi na iya sa mutane su fara tambayar ko da gaske ana yaƙi da cin hanci da rashawa ne, ko kuma ana amfani da shari’o’in wajen farautar abokan hamayyar siyasa.
Sanusi ya kawo batun tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma halatta kuɗaɗen da ba a san asalinsu ba.
Ya ce El-Rufai ya shafe watanni bakwai a tsare ba tare da an same shi da laifi ba, yana mai cewa an ƙi bayar da shi beli. Sai dai rahotanni sun nuna cewa batun belin El-Rufai ya kasance yana fuskantar wasu sharuɗɗa masu tsauri da suka kawo cikas ga sakin nasa.
Sanusi ya ce irin wannan lamari na iya sa jama’a su tambayi ainihin manufar da ke bayan wasu shari’o’in cin hanci da rashawa.
Ya ƙara da cewa ya kamata ’yan siyasa da hukumomin shari’a su tabbatar da cewa ana amfani da dokoki ne bisa manufar da aka kafa su domin cimmawa.
Sanusi ya ce duba da sake fasalin dokokin yaƙi da cin hanci abu ne mai kyau, amma ya kamata a kuma mai da hankali kan hukumomin da ke da alhakin aiwatar da waɗannan dokoki.
Ya ce idan ba a gyara yadda hukumomin da ke aiwatar da dokokin suke aiki ba, mutanen da ke da kyakkyawar alaƙar siyasa na iya ci gaba da tsallake wasu matakai na shari’a.
