Majalisar Wakilai za ta fassara dokoki zuwa Hausa, Igbo da Yoruba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar dokokin Nijeriya ta ce tana shirin fara fassara dokokin ƙasar zuwa Hausa, Igbo, Yoruba da sauran harsunan gida, domin sauƙaƙa wa jama’a fahimtar dokokin da suka shafi rayuwarsu.

Majalisar ta ce matakin na daga cikin shirye-shiryen amfani da fasahar zamani wajen inganta hanyoyin da jama’a ke samun bayanai kan ayyukan majalisa da dokokin ƙasa.

Haka kuma, Majalisar na shirin ƙaddamar da manhajar wayar hannu ta National Assembly Library, wadda za ta bai wa jama’a damar samun bayanan majalisa cikin sauƙi.

Za kuma a kafa Bills Tracker, domin bai wa jama’a damar bibiyar matakan da kudurorin doka ke bi tun daga gabatar da su har zuwa amincewa ko kin amincewa da su.

Baya ga haka, Majalisar ta ce za ta samar da hotuna, bidiyoyi da sauran bayanai cikin salo mai sauƙin fahimta, domin ƙara wayar da kan jama’a kan dokoki da tsarin gudanar da majalisa.

Jami’an Majalisar sun kuma bayyana shirin ƙarfafa tsaron bayanan majalisa, musamman domin kare su daga satar bayanai, sauya takardu ba tare da izini ba da kuma yaɗa takardun bogi.

Sun ce amfani da fasahar zamani da basirar wucin gadi (AI) zai taimaka wajen inganta bincike da sauƙaƙa samun bayanan majalisa, sai dai sun jaddada buƙatar tabbatar da sahihancin bayanai, tsaronsu da kuma ingancinsu.

By ukarofi

Leave a Reply