Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani bincike da Premium Times ta gudanar kan wata ɗoyayyiyar yarjejeniya a ƙasashen ketare da ta shafi iyalan tsohon mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, da ɗan kasuwa Leno Adesanya, ya taimaka wa Gwamnatin Nijeriya wajen samun nasara a rikicin aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.
Binciken, wanda aka wallafa a ranar 13 ga Oktoba 2021 a matsayin wani ɗangare na aikin Pandora Papers, ya zama cikin hujjojin da Gwamnatin Nijeriya da lauyoyinta suka gabatar yayin shari’ar sasantawa a Kotun Kula da Harkokin Kasuwanci ta Duniya (ICC) da ke Paris, Faransa.
Binciken ya bankaɗo bayanai kan wani kamfani mai suna Hydropower Investments Limited, wanda aka kafa domin ’ya’yan Dasuki uku tare da tsara shi domin riƙe hannun jari a wasu kamfanonin da ke da alaƙa da Adesanya, ciki har da Sunrise Power & Transmission Company Limited, kamfanin da ke tsakiyar rikicin aikin Mambilla.
Premium Times ta gano cewa an kafa Hydropower Investments a British Virgin Islands ranar 14 ga Nuwambar 2013 ta hannun kamfanin kula da kadarorin ƙasashen ketare na Trident Trust Company Limited. Adesanya da Abubakar Atiku Dasuki ne daraktocin kamfanin.
Masu cin gajiyar hannun jarin kamfanin guda uku su ne Abubakar Atiku Dasuki, Hassan Sultan Dasuki da Asmau Iman Dasuki, waɗanda duk ’ya’yan tsohon mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, ne.
An tsara kamfanin ne domin riƙe hannun jari miliyan 10 na kamfanin Sunrise Power da kuma miliyan 1.5 a Sino Africa.
Binciken bai samu wata shaida da ke nuna cewa ’ya’yan Dasuki sun biya kuɗin hannun jarin ba. Lokacin da Trident Trust ta tambayi yadda za a samar da kuɗin sayen hannun jarin, Adesanya ya bayyana cewa za a shirya kuɗin ne ta hanyar wani bashi daga mai ɗaukar nauyin aikin.
Binciken ya kuma gano cewa Adesanya ya ci gaba da kasancewa babban mai hulɗa da kamfanin, inda aka yi amfani da gidansa da ke Legas a matsayin adireshin kamfanin.
Adesanya, ta hannun wakilinsa, ya musanta samun wata alfarma daga Dasuki, yana cewa kawai ya taimaka wa ’ya’yan tsohon mashawarcin shugaban ƙasar ne domin fara kasuwanci. Shi ma Dasuki ya musanta neman Adesanya ya kafa kamfanin domin ’ya’yansa.
Kotun ICC ta kuma binciki wani kuɗi da aka biya na Dala miliyan 1.74 da Adesanya ya yi wa Abubakar Dasuki a watan Disambar 2014. Kotun ta yi watsi da bayanin Adesanya cewa rancen kuɗi ne, tana mai cewa akwai saɗani tsakanin bayaninsa da sauran hujjojin da aka gabatar.
“Kotun ba ta gamsu da bayanin Adesanya kan kuɗin rancen na Dala miliyan 1.74 ga Dasuki ba saboda rashin daidaito tsakanin asusunsa da sauran sassa na ajiyayyun bayanai ba,” inji kotun.
Kotun ta kuma tambayi dalilin da ya sa ba a rubuta yarjejeniyar rancen kuɗin ba, tana mai cewa kamfani kamar Sunrise, wanda ke samun wakilcin ƙwararren ɗan kasuwa kamar Adesanya, ya kamata ya riƙa rubuta irin waɗannan mu’amaloli na kasuwanci.
Kotun ta lura cewa wanda ya karɗi kuɗin ɗan Sambo Dasuki ne, wanda ya riƙe muƙamin mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro daga watan Yunin 2012 zuwa Yulin 2015.
Kotun ta ce biyan kuɗi ga ’yan gidan wani jami’in gwamnati na iya zama cin hanci, kamar yadda dokokin yaƙi da cin hanci na Nijeriya suka tanada. Sai dai kotun ba ta gano cewa biyan Dala miliyan 1.74 na da alaƙa kai tsaye da aiwatar da yarjejeniyar aikin Mambilla ba, duk da cewa ta ce mu’amalolin sun ƙunshi manyan alamomin tuhuma.
Kotun ta kuma ambaci binciken Premium Times kai tsaye lokacin da take nazarin zargin Nijeriya cewa an karkatar da wani kaso na hannun jarin Sunrise Power zuwa ga ’yan gidan Dasuki ta hanyar kamfanin Hydropower Investments.
Kotun ta bayyana cewa Nijeriya ta danganta zargin nata da wasu takardu da suka fito fili bayan ɗullar bayanan Pandora Papers, tare da ambaton rahoton Premium Timesa matsayin tushen hujjar.
Premium Times ce kaɗai daga cikin jaridun Nijeriya da ta shiga cikin wannan gagarumin binciken Pandora Papers na duniya, wanda International Consortium of Investigatiɗe Journalists (ICIJ) ta jagoranta.
Daga baya lauyoyin Nijeriya sun tuntuɗi Premium Timesdomin neman ƙarin bayanai da takardu kan binciken. Jaridar ta ba su rahoton da takardun da ke tare da shi, waɗanda aka yi amfani da su a matsayin wani ɗangare na hujjojin shari’ar.
Bayan hukuncin, babban editan Premium Times, Idris Akinbajo, ya ce jaridar ta yi farin ciki kuma tana alfahari da ta taimaka wajen nasarar Nijeriya a shari’ar.
A cewarsa, jaridar za ta ci gaba da yin dukkan ƙoƙarin da za ta iya wajen ɗaga darajar Nijeriya, yankin Afirka da kuma al’umma baki ɗaya.
A hukuncin da ya shafi rikicin Mambilla, kotun ICC ta yi watsi da manyan buƙatun Sunrise Power da Leno Adesanya, sannan ta umarci kamfanin da Adesanya da kansa su biya Nijeriya wani kaso mai yawa na kuɗaɗen shari’a da aka kashe. Premium Timesta ce da Nijeriya ta yi rashin nasara, da kuɗin da take fuskantar biyan wa a ƙarƙashin buƙatun shari’ar sun iya kai sama da Dala biliyan uku.
