Matatar Dangote ta kai kashi 105 na ƙarfin aiki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar Dangote ta gudanar da aiki sama da cikakken ƙarfinta a watan Agustan 2026, inda ta kai kashi 105.21 cikin 100 na ƙarfin samar da mai, yayin da shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu da kashi 26 cikin 100.

Hakan na ƙunshe ne cikin takardar bayanan watan Agustan 2026 da Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta fitar, wadda aka raba wa ’yan jarida ranar Alhamis.

Bayanan sun nuna cewa matatun mai na cikin gida sun karɓi matsakaicin ganga 683,000 na ɗanyen mai a kowace rana, wanda ya nuna ƙarin kashi 17 cikin 100 daga ganga 585,000 da aka samu a watan Yuli. Jimillar man fetur da aka karɓa ta aaru da kashi 11 cikin 100, daga lita miliyan 45.5 zuwa lita miliyan 50.5 a kowace rana.

A cikin wannan adadi, samar da man fetur daga cikin gida ya ƙaru da kashi 39 cikin 100 zuwa lita miliyan 35.9 a kowace rana, yayin da shigo da shi daga ƙasashen waje ya ragu daga lita miliyan 19.7 zuwa miliyan 14.6 a kowace rana.

Matatar Dangote ta samar da matsakaicin lita miliyan 41.94 na man fetur a kowace rana, inda ta samar da lita miliyan 35.87 ga kasuwar cikin gida tare da fitar da lita miliyan 9.73 zuwa ƙasashen waje.

Haka kuma, matatar ta samar da lita miliyan 18.01 na dizal da kuma lita miliyan 24.48 na man jiragen sama a kowace rana. Daga cikin waɗannan, ta fitar da lita miliyan 8.75 na dizal da kuma lita miliyan 21.30 na man jiragen sama zuwa ƙasashen waje.

A ɓangaren dizal kuwa, yawan man da aka karɓa ya ragu da kashi 39 cikin 100, daga lita miliyan 23.6 zuwa miliyan 14.5 a kowace rana. Shigo da dizal daga ƙasashen waje ya ragu da kashi 84 cikin 100 zuwa lita miliyan 1.3 a kowace rana, yayin da dizal da aka samar a cikin gida ya ragu da kashi 16 cikin 100 zuwa lita miliyan 13.2. Adadin dizal da ake da shi a rumbu ya inganta, inda ya kai abin da zai iya ɗaukar kwanaki 51.6, daga kwanaki 46.5 a watan Yuli.

Amfani da man fetur, wanda aka auna ta yawan man da aka fitar daga wuraren rarrabawa domin kai shi kasuwa, ya ragu da kashi 14 cikin 100, daga lita miliyan 48.3 zuwa miliyan 41.5 a kowace rana. Haka kuma, yawan man fetur da ke akwai a ajiya ya ɗan ƙaru zuwa abin da zai iya ɗaukar kwanaki 22.9, daga kwanaki 22.4.

A ɓangaren man jiragen sama kuwa, yawan man da aka karɓa ya ƙaru da kashi 63 cikin 100 zuwa lita miliyan 3.1 a kowace rana, yayin da amfani da shi ya ƙaru da kashi 22 cikin 100 zuwa lita miliyan 2.8 a kowace rana.

Yawan iskar gas ɗin girki, wato LPG da aka karɓa ya ragu da kashi 19 cikin 100 zuwa tan 4.3 a kowace rana, yayin da samar da shi a cikin gida ya ragu da kashi 32 cikin 100, amma shigo da shi daga ƙasashen waje ya ƙaru da kashi 44 cikin 100. A halin da ake ciki, matatun mai na Kamfanin Mai na ƙasa na Nijeriya (NNPCL) da ke Fatakwal, Warri da Kaduna ba sa samar da mai.

Daga cikin ƙananan matatun mai masu zaman kansu, matatar Edo ta yi amfani da kashi 90.43 cikin 100 na ƙarfin samarwarta, Walter Smith kashi 64.77, Aradel kashi 58.77, yayin da OPAC ta yi amfani da kashi 16.97. Ita kuwa matatar Duport tana rufe.

A ɓangaren iskar gas kuwa, samar da iskar gas na cikin gida, ciki har da adadin da ake bai wa kamfanin NLNG, ya ƙaru da kashi huɗu cikin 100, daga ƙafa biliyan 4.723 zuwa biliyan 4.930 a kowace rana. Daga cikin wannan adadi, an ware ƙafa biliyan 0.537 na iskar gas a kowace rana domin samar da wutar lantarki.

By ukarofi

Leave a Reply