Atiku ya buƙaci Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashi saboda tsadar rayuwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa, yana mai cewa albashin Naira 70,000 da ake biya a yanzu ya rasa ƙarfinsa sakamakon tsadar man fetur da hauhawar farashin kayan masarufi.

Atiku ya kuma goyi bayan buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago na neman ƙarin albashi mai tsoka, yana mai cewa ma’aikata na fuskantar wahalar biyan sayen abinci, sufuri, haya da sauran muhimman buƙatun rayuwa.

Daraktan Sadarwa da Tsare-tsaren Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ne ya bayyana matsayin Atiku a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya soki yadda ƙarin farashin man fetur ke ƙara wa ma’aikata wahala.

Atiku ya ce, idan aka yi la’akari da farashin litar man fetur da ya kai Naira 1,400, albashin mafi ƙarancin Naira 70,000 a wata zai iya sayen lita 50 ne kawai. Ya tambayi abin da ma’aikacin zai yi da sauran buƙatun rayuwa bayan ya kashe kuɗinsa wajen sayen man fetur, yana mai cewa akwai buƙatar a yi la’akari da yadda ma’aikata za su ciyar da iyalansu, biyan haya da kuma samun kuɗin da za su koma wuraren aikinsu.

Atiku ya kwatanta albashin mafi ƙarancin Naira 70,000 da tsohon albashin Naira 30,000, yana mai cewa ƙarin albashin bai haifar da ƙaruwa mai ma’ana a ƙarfin sayen kayayyaki ba saboda tsananin hauhawar farashi. Ya ce, a watan Afrilun 2023, lokacin da matsakaicin farashin litar man fetur ya kai Naira 254.06, albashin Naira 30,000 zai iya sayen kusan lita 118.

Sai dai a yanzu, in ji shi, albashin Naira 70,000 a kan farashin Naira 1,400 na iya sayen lita 50 kacal. Atiku ya ce, duk da cewa adadin albashin da ke cikin takardar biyan ma’aikaci ya ƙaru, yawan man fetur da albashin zai iya saya ya ragu da fiye da rabin abin da yake iya saya a baya. Ya bayyana cewa aarin albashin bai wadatar wajen rage wa ma’aikata raɗaɗin tsadar rayuwa ba, saboda farashin man fetur, abinci, sufuri da haya sun tashi sosai.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma ɗora wani ɓangare na matsin tattalin arzikin da ma’aikata ke fuskanta kan cire tallafin man fetur, yana mai cewa tashin farashin mai ya haifar da ƙarin kuɗin sufuri tare da ɗaga farashin sauran kayayyaki da ayyuka. Atiku ya ce, tasirin farashin man fetur bai tsaya kan kuɗin sufuri kawai ba, domin tsadar makamashi tana shafar noma, harkokin kasuwanci da kuma kuɗaɗen da iyalai ke kashewa a rayuwarsu ta yau da kullum.

A cewarsa, farashin man fetur yana ratsawa kusan kowane sashe na tattalin arziki; yana ƙara kuɗin da manomi ke kashewa wajen kai amfanin gona kasuwa, yana ƙara kuɗin sarrafa abinci a masana’antu da gidajen burodi, sannan ya bayyana a cikin kuɗin da iyaye ke biya wajen kai ’ya’yansu makaranta.

Atiku ya kuma kwatanta mafi ƙarancin albashin Nijeriya da na wasu ƙasashen Afirka, inda ya kawo alkaluman da suka nuna cewa albashin da ya yi daidai da na Nijeriya ya kai kusan Naira 213,000 a Libya, Naira 245,000 a Aljeriya, Naira 302,000 a Eƙuatorial Guinea, da kuma Naira 351,000 a Gabon, bisa farashin canjin kuɗin da ya yi amfani da su.

Sai dai ya amince cewa tsarin albashi da kuma tsadar rayuwa sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, amma ya dage cewa Naira 70,000 bai wadatar da ma’aikatan Nijeriya ba bisa la’akari da irin farashin kayayyaki da ake fuskanta a yanzu.

Atiku ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sake tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikata domin samar da ƙarin albashi mai ma’ana wanda zai yi daidai da yanayin tsadar rayuwa.

Ya kuma yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban ƙasa a shekarar 2027, zai ƙara mafi ƙarancin albashi tun daga farkon mulkinsa, tare da aiwatar da wasu matakai da ya ce za su rage wa ma’aikata matsin tattalin arziƙi.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa farashin litar man fetur ya kai kusan Naira 1,400 a Legas da Abuja, yayin da wasu sassan Arewacin Nijeriya ke sayar da litar da kusan Naira 1,500.

Sabunta muhawarar kan mafi ƙarancin albashi na zuwa ne a daidai lokacin da tashin farashin man fetur ke ci gaba da matsawa aljihun iyalai, tare da ƙara tsadar sufuri da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum.

By ukarofi

Leave a Reply